AN SACE MUTANEN SOKOTO
daga jaridar sokoto
Daga Hanyar Gombe Zuwa Sokoto: An Dauke Fasinjoji Har Direban Mota Su 13 ‘Yan Asulin Jahar Sokoto.
Rahotanni sun tabbatar da cewar, wasu gungun ‘yan bindiga sun tare wasu ma tafiya ‘yan asulin jihar Sokoto su goma sha uku 13 a hanyar Sheme zuwa ‘Yan Kara ta jihar Katsina inda suka yi Garkuwa dasu.
Lamarin wanda ya faru da marecen ranar jiya assabar 19 ga watan Yuni 2021, daidai lokacin da fasinjojin ke kan hanyar tafowa sokoto bayan sun taso daga jihar Gombe.
Shaidun gani wa ido sun tabbatar da cewar, an dauki fasinjojin ne har direba kuma ana kyautata zaton dukkan su ‘yan jihar Sokoto ne dake arewacin Najeriya.
“Ana Neman Al’ummar Musulmi Su Sanya Wadannan Ma Tafiyan Cikin Addu’ar Su, Don Samin Nasarar Kubucewa daga Hannun ‘Yan Bindigar”
Jaridar Sokoto