WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?

0

 

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?

. ..Siyasar Zaben 2023

Mu’azu Hassan
@ Katsina City News

Yanzu saura shekara daya da watanni a yi sabbin zabubbakan a kasar nan, gwamnatoci na Jihohi da Tarayyar suna ta ayyukan da za su bar tarihi.

Sama da shekara daya da suka gabata, Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya yi wani gargadi a Karamar Hukumar Zango da ke yankin Daura, inda ya yi kira ga masu rike da mukaman gwamnati su mai da hankalinsu a kan yi wa jama’a aiki, ba neman tallata niyyarsu ta takara ba.

A wani wuri har yana cewa wanda ke neman tallata kansa ya ajiye masa mukaminsa ya ba wanda zai sanya harkar jama’ar Katsina gabansa.

Gwamnan ya sake maimaita wannan maganar a wani taro da aka yi da shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Katsina baki daya a Eagle Square.

A taron, Bala Abu Musawa, mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na Funtua shi ne ya fara jawo hankalin masu rike da mukaman jam’iyya a kan goyon bayan wani dan takara.

Gwamnan Katsina na fara magana ya goyi bayan Bala Abu Musawa, ya kuma maimaita gardadin can da ya taba yi a Karamar Hukumar Zango.

Siyasa mataki-mataki ce, akwai ganawa da tattaunawa a gefe da taron sirri da fadin niyya ga wadanda suka zo wajenka jin ra’ayinka.

Akwai kuma gangami da jerin gwano da taron bayyane da buga fastoci kala-kala.

A iya bincikenmu a duk fadin kasar nan, mai Jihohi 36, babu inda wani da ke a cikin gwamnati ya fito yana ayyukan neman takarar Gwamna kamar Katsina.

Domin wannan binciken mun buga mun yi binciken Jiha bayan Jiha, ko’ina amsar daya ce, babu wanda yake rike da mukami a cikin gwamnatin Jaha , kuma yana ayyukan da aka tabbatar ta neman takara ce. Duk Nijeriya babu sai a Katsina. In kuma akwai .jaridar nan na bukatar a kawo mata a rubuce da hujjojin hakan

Gwamnan Katsina ya yi gargadin a bayyane har sau biyu, ya yi a gefe ya fi sau shurin masaki.

Amma wani wanda kowa ya san karfinsa a cikin gwamnatin da ke mulkin jahar nan, yana ayyukan da kowa ya san ina suka nufa.

Ana tarurruka da buga riguna da ba da gudummuwar kudi ga ibtilai, an fara fentin gidaje da sanya wa motoci hotuna duk da sunan wani mai neman takara.kuma mai rike da kujera a gwamnatin jahar.

Tambayiyo uku masu ”ya ‘ya wasu ke yi, inda suke cewa, ya kamata a ba da amsar ;
(1) wa ke ba da kudin daukar dawauniyar duk wadannan? A ina aka samo kudin?
Waya ba da kudin motocin da wani wanda kowa ya san waye shi? Ya ce wai ya lika ma hotuna?

Daga ina kudaden da ake tarurruka ke fitowa? Wanda kowane taro ana kashe miliyoyin Naira?
Fastoci da riguna da ake ta tallar an buga wa ya biya su?

Wasu da ake ta biyan kudin data suna rubutu ba ji, ba gani, wa ke biyansu?

Kudaden da lissafin da ake aiki da su suna da yawan gaske, daga ina suke fitowa? Wani dan kasuwa ne, ko wani jami’in gwamnati, ko ko wani asusu aka fasa yanzu ake aiki da su?

Tambaya ta biyu shin wannan aikin da ake yi bai saba wa umurni da gargadin da Gwamnan Katsina ya yi a bayyane har sau biyu ba?

Me ya sa duk Nijeriya sai Katsina ce kawai wannan ke faruwa?

Wa aka raina? Gwamnan Katsina, ko jam’iyyar APC ta Jiha?

Tambaya ta uku kuma ta karshe, shin damuwar ‘yan Katsina da halin da take a ciki na maharan daji da rashin noma a wasu yankunan ya kamata a mai da hankali yanzu, ko ko a’a?

Shin nauyin da aka dora wa mutumin da ke cikin gwamnatin ya kamata ya mai da hankalinsa, ko kokarin takara?

Shin mai wannan aikin ko ya fi karfin kowa ne? Ko ko bai jin magana ne? Ko bai jin shawara ne? In kuma haka ne halinsa ya cancanta ya yi takara ko da ta Kansila ce? Ya can canta a bishi tunda shi yaki yin biyayya?

Wadannan tambayoyin na damun wasu masu kishi da makomar Katsina.
Kuma lokaci yayi da gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello masari zai bayyana matsayin shi akan wannan! In an bude kofa ne a sani.in kuma rashin girmamawa na gaba ne shima a sani…
TUN WURI, KAFIN LAMARIN YA KARA LALACEWA..

Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Katsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here