BIYAN TSAFFIN SHUGABANNIN KANANAN HUKUMOMIN KATSINA.

0

SABON RIKICI:
BIYAN TSAFFIN SHUGABANNIN KANANAN HUKUMOMIN KATSINA.
~Mun fara biyan wasu…Masari

~Ba Wanda aka biya. …Majigiri

Sulaiman Umar
@Jaridar Taskar Labarai

A wata ganawa da gwamnan Katsina yayi da manema labarai kwanakin baya.
Yace gwamnatin sa za ta mutunta hukuncin babbar kotun kasa na biyan duk wadanda tace a biya.

Gwamnan yace amma yanzu suna jiran amsar cikakken hukunci kotun su karanta don aiki da abin da kotun tayi umurni daki-daki.

Gwamnan ya ce sun riga sun tattara duk abin da ya kamata su biya a bangaren gwamnati.

Gwamnan ya daga wani kundi a gaban yan jaridun yace bayanin komai na biyan tsaffin jami’an na kananan hukumomin yana a cikin wannan.

Gwamnan ya kara da cewa, da ma mun riga mun fara biya. Gwamnan yace muna da lissafin duk abin da muka biya, da abin da zamu karasa.

Amma a wata hira da Jaridar Taskar Labarai tayi da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Alhaji salitsu Yusufu Majigiri cewa yayi su a iya sanin su da kuma doka sam ba wanda aka biya ko sisi.

Yace shi ya sanya suka kafa kwamiti karkashin jagorancin Ibrahim Lawal Dankaba, kuma kwamitin ya basu rahoton abin da gwamnatin jiha zata biya su, yace sun kuma mika rahoton su ga gwamnatin jiha da lauyoyinsu.

Majigiri yace jam’iyyar PDP ce ta kai kara, kuma a karar cewa take a mai da zababbun ta bisa mulki.

Ba inda suka ce suna bukatar kudi a hukuncin kotu tace a bada kudi don haka jam’iyyar PDP za a ba kudi ta raba ma zababbunta.

Majigiri yace, ba wani da ya kai kotu shi daya, don haka in gwamnati tayi magana da wani tayi ne bisa radin kanta, kuma ba bisa tsari da doka ba.

Majigiri yace kudin mu zamu amsa cas, babu kankaren ko taro sai mun kirga, mun tusa gaban shaidu, sannan mu amince.

In kuma aka samu akasin haka zamu koma ma babbar kotun kasa inji Majigiri.

Jaridar Taskar Labarai ta samu tabbacin lallai da yawan zababbun sun amshi kudade a wajen gwamnati. Kudin da Majigiri yace su dauka sun ci bilis.

Wannan sabon rikicin ba a san yadda za a karkareshi ba.

Asalin dai rikicin kananan hukumomi ya faro ne daga zaben 2015 inda gwamnatin jiha baki daya jam’iyyar APC ta lashe amma a kananan hukumomi akwai zababbun ciyamomi yan jam’iyyar PDP.

Ance a lokacin, ra’ayi ya rabu biyu gwamnan Katsina a lokacin yana son a kyale ciyamomin su kammala wa’adinsu, wanda saura watanni kadan.

Wasu ma sun yi niyyar komawa jam’iyyar ta APC a lokacin.

Wani mutum mai karfi a tafiyar, ya dage sai an rusa su hatta wani kwamitin bada shawara a shari’ance ya jawo hankalin mutumin can cewa, akwai sarkakkiyar shara’a idan ka rusa su, in ka rusa ciyamomi ya zaka yi da mataimakansu balle kansilolinsu?

Baka iya yi masu kudin goro baki daya kace sun yi laifin kora.

Mutumin can ya kafe ya kuma rinjayi kowa a cikin gwamnatin kamar yadda wata majiya ta shaida mana.Sai da aka rusa.wannan mataki shine ya kai jahar katsina halin da take ciki a yanzu.
Ita kuma jam’iyyar PDP ta kai kara a kotu suka raba Shari’ar kashi-kashi. Suka damalmala lamarin.

Kotun farko ta tarayya mai zaman ta Katsina ta ba gwamnatin jiha goyon baya, kotun daukaka kara dake Kaduna itama taba gwamnatin jiha gaskiya, amma kotun tarayya ta kasa ta hada duk shari’un waje daya ta kuma yanke hukuncin cewa an rusa kananan hukumomin ba bisa kaida ba.

Don haka, a biya jami’an da aka kora hakkokinsu baki daya.kuma ba laifin da sukayi.

Yanzu akan biyan hakkokin ake wanda gwamnatin jiha ta amsa zata bi umurnin kotun.

Jaridar Taskar Labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina City News
Www.katsinacitynews.com
The Linke News
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245.
Katsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here