AN KAI HARI GA MA AIKATAN KIDAYA A BATSARI JAHAR KATSINA

0

AN KAI HARI GA MA AIKATAN KIDAYA A BATSARI JAHAR KATSINA
Misbahu Ahmad batsari
@ jaridar taskar labarai
Da yammacin ranar jumaa 02-07-2021 wasu mahara dauke da miyagun makamai suka zagaye kauyen Dogon Hako dake cikin yankin karamar hukumar Batsari jahar katsina.
Wani da al’amarin ya rutsa dashi ya bayyana ma jaridun taskar labarai cewa da misalin karfe 01:30 Rana suna cikin kauyen,ana aiki.
Sai suka ji karar bindigu na tashi ta ko wane bangaren garin. Lokacin kuwa akwai masu aikin shata iyaka cikin garin, suna ta aikin su tare da rakiyar motocin jami’an tsaron ‘yan sanda da ‘yan banga.harin yasa kowa ya kidume yana neman mafita, gashi kuma sun zagaye kauyen.
Haka dai aka samu hanyar arcewa inda wajen gudu wasu daga cikin masu neman tsira suka haye ma maharan, har suka harbi wani dan banga a kafa. mai suna Musab kura. Sai dai duk da raunin ya sha da raunin harbin da sukayi masa.
Ganau sun bayyana ma jaridun taskar labarai cewa, maharan wadanda ake da tabbacin barayin daji ne sun kona motoci guda ukku ciki har da motar jami’an tsaro.
Daga bisani dai aka sake tura wasu jami’an tsaro domin kubutar da ma aikatan, kuma anyi nasarar hakan.

Musan kura da aka harba a kafa

Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779.08137777246
Katsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here