GWAMNA BAI DA DAN TAKARA

0

GWAMNA BAI DA DAN TAKARA

Inji Alhaji Muntari Lawal
……ZA A FARA FITO NA FITO
___ inji majiya mai tushe

Muazu Hassan
@Katsina City News

Jigo a jam’iyyar APC kuma shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina Alhaji Muntari Lawal ya bayyana cewa gwamnan Katsina baya da wani dan takara na neman mukamin gwamna kuma bai aiki kowa ga jama’a ba don ayi tallar wani dan takara.

Alhaji Muntari Lawal na wannan jawabin ne ga shugabannin kamfen gwamnan Katsina Aminu Bello Masari na kananan hukumomi talatin da hudu na jahar Katsina.

Majiyoyi daban-daban da suka tabbatar ma da Katsina City News labarin sun ce, Alhaji Muntari Lawal ya gayyato wadannan shugabannin ne a ofis din sa dake gidan gwamnatin Katsina a ranar laraba 29/Yuni/2021. Inda ya jawo hankalin su akan yadda wadansu ‘yan takara na neman gwamna ke tafiya kananan hukumomi suna ganawa da mutane kuma suna karyar cewa dan takarar da suke talla shi ne wanda gwamnati da gwamnan Katsina ke mara wa baya.

Alhaji Muntari Lawal yace abin da ake yi cin fuska ne ga gwamnan kuma rashin kula ne da hakkin jama’a da aka dora mana.

Alhaji Muntari Lawal wanda yana daya daga cikin jiga jigan kamfen din APC ya jawo hankalin wadannan ko’odinotocin na kamfen Masari akan karya da sunan gwamnati da gwamnan Katsina don tallata kowane dan takara.

Ya kuma ce masu sako ne, Wanada yaji ya je ya fada ma wanda bai ji ba, ya kara da cewa abin da ke gaban gwamnatin nan daga sauran kwanakin da suka rage mata aiki.

Cikin fushi yace a yanayin nan raini ne kuma rashin adalci ne ga mai girma gwamna a dauke hankalin al’umma da maganar dan takara, kuma ba zamu bari ba.
Alhaji Muntari Lawal yace muna sane da yadda wasu ma’aikatan gwamnati suka shiga tsundum a wannan abin da bai dace ba.
Alhaji Muntari Lawal yace mu ke bisa mulki muna da shugaba kamata yayi a jira ya tsara mana lokacin da za ai komai bisa tsari.

A wata sabuwa wasu na kusa da gwamnan Katsina masu rike da mukaman siyasa sun tsara ma kansu zasu fara fita kwararo-kwararo lungu sun wayar wa da jama’a kansu cewa, a yanzu gwamnan Katsina ta aikin shi yake ba dan takara ba, kuma duk wanda yace an aiko shi shi ne dan takara karya yake.

Wani jigo a tafiyar ya fada wa jaridun Katsina City News cewa, “mun tsara da kudin kan mu ba wanda ya sanya mu. Duk inda suka je suka fada zamu je muma mu fadi, rashin jin kunyar maras kunya halas ne”.

A Katsina masu neman takarar gwamna suna da yawa, amma kowanne su sun tsaya ne a tuntuba da tattaunawa wanda wannan ba wani abu bane.

Mutum daya shi ne yafi zakewa kuma yana da mukami a cikin gwamnatin ana taruka a ofishin jam’iyya na jiha don tallata shi, wasu da ake ganin na kusa da shi ne masu rike da mukaman siyasa ana zargin suna amfani da kujerun su don tallata shi.

Mafi muni wani babban sakataren wata babbar ma’aikata da ya tsunduma tsundum wajen harkokin tallar shi duk da kuwa mukamin babban sakatare mukamin aiki ne bana siyasa ba, wanda har an fara zargin daga wannan ma’aikatan ake daukar nauyin tallar wancan dan takarar.

Binciken Taskar Labarai ya gano duk Nijeriya a jihar Katsina ne kawai wani dake cikin gwamnati da mukamin siyasa ya fito karara yana neman takara a 2023.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245
email katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here