Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Ma’aikata Na Jihar Katsina (1}
Bayan gaisuwa da fatan alheri. Na rubuto maka wannan wasikar ne domin in jinjina maka a kan yadda ka kawo da’a, cigaba da natsuwa a aikin gwamnati a Jihar Katsina.
Na biyu kuma in tambaye ka, shin mukamin Babban Sakatare na Ma’aikatar Kananan Hukumomin Katsina na siyasa ne?
Shin Babban Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomin Katsina ya fi karfin doka ne?
Me ya sa aka kyale shi yake ayyukan siyasa da tallar dan takara tun yanzu? Koko tsarin aikin gwamnati ya amince mai mukami irin nasa ya hada aikinsa da tallar siyasa?
Yallabai, ina neman amsar wadannan tambayoyin kafin in yi wasu a rubutun wasika ta gaba.
Babban Sakatare na Ma’aikatar Kananan Hukumomin Katsina yana shugabantar wata kungiya mai suna MUSTAFA INUWA ALHERI NE, wadda ke da muradin ganin Mustafa Inuwa ya kai gaci a zaben Gwamna a 2023.
Yana kuma kokarin jawo ra’ayin ma’aikatan Kananan Hukumomi su mara masa baya.
Kuma yana neman fifita wannan aikin fiye da aikinsa na ofis.
Ko a ranar Asabar 3/7/2021 ya yi taro a Funtua. A taron mafi yawan wadanda suka halarta ma’aikatan Kananan Hukumomi ne, ciki har da masu rike da shugabancin mulki da kudi na Kananan Hukumomi.
A wasikar nan na hada maka da hotunan taron, inda ya fito muraran.
Wannan dabi’a ta Babban Sakatare, dabi a ce mafi hatsari a aikin gwamnatin Katsina, wanda in ba a yi maganinta da wuri ba, za ta iya zama wata nakiya mai illar gaske.
Wannan wasikar a gare ka ta farko ce, kuma za ta cigaba har sai an yi wa tufkar hanci.
Da fatan zan samu amsa kafin in saki wasikata ta biyu gare ka.
Daf na Kankara.Alhaji sule funtua.
Hotuna; yadda ma aikatan kananan ke tarayyar babban sakataren ma aikatan kananan hukumomin katsina
*Abdul Aziz Abdullahi*
*Chairman*
*Katsina State First Initiative.*
*No 55 IBB Way Katsina*
Note;;
Wannan wasikar da turanci aka rubuta. Jaridar taskar labarai; suka fassara zuwa harshen Hausa.
Www.jaridartaskarlabarai.com.