KUNGIYA A BATSARI; TA KARRAMA JAGORORIN TSARO.

0

KUNGIYA A BATSARI;
TA KARRAMA JAGORORIN TSARO.
@ misbahu Ahmad

A ranar lahadi 04-07-2021 wata kungiya mai fafatukar kawo cigaba a karamar hukumar Batsari mai suna Attau foundation ta karrama masu jagorantar tsaro a yankin da lambobin girma. Wadanda aka ba lambar yabon suna hada da DPO na Batsari, shugaban ‘yan banga, kwamandan sojoji da sauransu. An gudanar da wannan taro a sakatariyar karamar hukumar Batsari. A jawabin da ya gabatar, shugaban kungiyar Comrade Zaharaddeen Hamza, ya bayyana cewa bada wannan lambar yabo ya zama dole duba da yadda wadannan bayin Allah suka jajurce domin kare al’ummar karamar hukumar Batsari daga ta’addancin barayin daji, duk da cewa matsalar bata kare ba, amma dai kowa yasan irin kokarin da sukeyi wajen dakile hare-haren su.
Ya kara jinjina ga Sarkin Ruman Katsina hakimin Batsari Alhaji Tukur Muazu Rumah wajen goyon baya da hadin kai da yake badawa domin magance matsalar tsaro a kasar sa. Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kuma anyi taro an tashi lafiya.

See also  Sakamakon kira: Sojoji suna kama mutane da dama a katsina da zamfara

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here