UMAR TATA YA GANA DA JIKOKINSHI NA YANKIN DAURA

0

UMAR TATA YA GANA DA JIKOKINSHI NA YANKIN DAURA
Umar chroma
@ katsina city news
Alhaji Umar Tata gogaggen Dan siyasar nan da ya ke neman jam iyyar APC ta tsayar dashi takarar gwamna a shekarar 2023.ya gana da jikokinshi na shiyyar Daura kuma yayi masu kyaututtuka.
Jikokinshi wadanda aka Haifa da wani aikin Alheri da yayi a shekarun baya inda ya rika hada aure yana kuma yi ma ma auratan kayan Daki da biyan sadaki.
A lokacin Alhaji Umar Tata ya hada auren a shiyyoyi guda uku.funtua Daura da kuma katsina. Wanda za a hada ki da miji a biya sadaki.kuma ayi ma matar kayan daki.
A lokacin manyan malamai suka rika Daura aure a manyan masallatan jumma a na kowace shiyya.
A taron garin Daura Wanda akayi a filin kofar sarki na tsakiyar Daura Umar Tata an hada masa duk yaran da wannan aure ya samar.wadanda ya Kira da jikokinshi.
A taron jika dari da Saba in da bakwai ya halarta.tare da uwayensu.
Anyi jawabai,kuma anyi Raha da dariya na jika da kaka an kuma yi wasanni.wanda taron ya cika da Raha.
Umar Tata ya kuma raba kyaututtuka ga jikokinshi, wasu keke wasu kayan makaranta da jikka.ya kuma ba wasu uwayen kekunan din ki don su sami abin sana a.
A jawabin shi Umar Tata ya shelanta ya fito takarar gwamna a zabe mai zuwa na 2023.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here