MANSUR ALI MASHI YA KAFA KAMFANIN TAKI A MASHI

0

MANSUR ALI MASHI YA KAFA KAMFANIN TAKI A MASHI

@ Katsina City News

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mashi da Dutsi a Jihar Katsina, Alhaji Mansur Ali Mashi, ya kafa kamfanin taki a Mashi mai suna SAFALMA FERTILIZER.

Kamfanin, wanda yake gaf da shiga garin Mashi daga Katsina, ko in ka bar Mashi zuwa Katsina, an kafa masa katafaren mazaunin sa na dindindin.

A kwanakin baya ne daya daga cikin Editocin Katsina City News suka kai ziyarar gani da ido a wannan kamfanin, inda suka tarar an kafa manyan injuna na yin takin, har an fara fitar da buhunan takin na gwaji da kuma siyarwa.

Mazaunin na takin SAFALMA yana da sashen binciken kimiyyar takin da ofisoshi da kuma ma’ajiya daban-daban da isasshen filin ajiye manyan motoci ko kanana wadanda za su zo don daukar takin.

Kamfanin SAFALMA FERTILIZER ya samar kwararrun ma’aikatan da za su fitar da taki mai inganci babu amaja.

Shugaban kamfanin, Alhaji Mansur Ali Mashi, ya fada wa jaridun Taskar Labarai cewa: “Mun kafa kamfanin ne don samarwa da manoma taki mai inganci daga gida, kuma a samarwa da matasa aikin yi”.

Ya ce: “Duk takin da za mu fitar, za mu fifita Kananan Hukumominmu, sannan Jiharmu”.

Ya kara da cewa: “Taki ne daga gida, in ka ga matsala ka zo kamfanin ka yi korafi a gyara. Mun bude sashen sauraren ra’ayin manoma a kamfanin”.

Wannan shi ne kamfanin sarrafa takin zamani na uku da Mansir Ali Mashi ya bude. A baya ya kafa kamfanin casar shinkafa mai suna SAFALMA RICE da kamfanin tatsar mai da ake kira SAFALMA OIL. Duk suna kan titin Lawal Kaita Daura da Liyafa Otal Katsina.

Mansur Ali Mashi yana da katafaren wurin siyar da motoci manya da kanana mai suna SAFALMA MOTORS.

Ya kuma bude gidajen siyar da man fetur a Mashi da Dutsi mai suna IMAN and KAUSAR.

Kamar yadda bincikenmu ya tabbatar mana, sunan SAFALMA ya tsiro ne daga hada sunan Mahaifi da Mahaifiyar Mansur Ali Mashi. Gidajen siyar da mai kuma suna dauke ne da sunayen ‘ya’yansa guda biyu.

Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here