SANATA SADIQ YAR ADUA YA YI YAN DUBU DUBU A GIDANSHI

0

SANATA SADIQ YAR ADUA YA YI YAN DUBU DUBU A GIDANSHI
daga sirajo yandaki
Tsohon Sanatan shiyyar Katsina ta Tsakiya ya yi taron sada zumunci da wakilan shi da suka zabo wadanda suka amfana da sabon shirin Gwamnatin Tarayya na tallafa ma mutum dubu daya kowace karamar hukuma a fadin kasar nan.

Ranar Litinin 19/07/2021 tsohon Sanata da ya taba wakiltar shiyyar Katsina ta Tsakiya Sanata Sadiq Yaradua ya yi taron sada zumunci da da wakilan shi da suka zabo wadanda suka amfana da tallafin dubu sittin, sittin kalkashin sabon Gwamnatin Tarayya mai suna (SPW 774) reshen Jihar Katsina, wanda Ofishin karamin Ministan kwadago na kasa hadin gwiwa da Hukumar koyar da Matasa Sana’o’in hannu ta kasa suka bullo dashi.

Tunda farko da yake bayyana Makasudin taron mataimakin shugaban Kwamitin shirin na Jihar Katsina Alh. Musa Kankia yace” manufar taron domin sada zumunci da kuma ba Al’umma hakuri akan yadda shirin yake tafiya, na jinkiri da ake samu wajen turama jama’a kudaden, Ya cigaba da cewa” Bankuna na nan na iya bakin kokarinsu akan shirin domin ganin sun turama jama’a kudadensu, kuma da iznin Allah sai kowa yaji “Alert” na shigar kudaden, saboda haka a kara hakuri kadan komi zai zama tarihi.

Shima a nashi jawabin Sanata Sadiq Yaradua ya bayyana cewa” ya kira wannan taro ne domin ya sada zumunci ga wadannan Al’umma da sukeyi mashi fatan alheri, ya kuma bada hakuri akan yadda ake samun tsaiko wajen biyan kudade na wannan sabon shirin Gwamnatin Tarayya na bada tallafin dubu sittin, sittin ga mutum dubu daya a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomi (774) na fadin Nigeria baki daya.

Sanata Sadiq Yaradua shine ofishin karamin Ministan kwadago hadin gwiwa da hukumar koyar da Sana’o’in hannu ta kasa suka ba alhakin kula da shirin a Jihar Katsina, da ya tabo bangaren siyasa kuwa, Sanata Sadiq Yaradua yace” yanata samun kiraye, kiraye daga jama’a da dama akan batun ko zaiyi takara 2023 ko bazaiyi ba? Sanata Sadiq Yaradua saiya kada baki yace” akan kiraye, kirayen da jama’a suke tayi mashi na maganar tsayawa takara 2023.

Sanatan ya cigaba da cewa” a halin yanzu bayada sukunin yin tsayawa wata takara tukuna, amma idan ya samu sukuni nayin takara zaiyi takara, haka zalika Sanatan yace” kafin ma mutum ya fara tunanin wata takara yana da kyau mu bari jam’iyyar ta zauna da gindinta, sanin kowa ne a halin yanzu jam’iyya na shirye, shiryen zabar shugabanninta tun daga matakin mazaba zuwa matakin Tarayya.

Daga karshe Sanata Sadiq Yaradua ya yaba ma Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari akan yadda ya yi kokari wajen kafa Kwamitin dazai gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar Apc a Jihar Katsina tun daga matakin mazaba zuwa matakin Tarayya, haka zalika Sanatan ya nuna jin dadin shi akan yadda Gwamnan ya zabo mutunen kirki mai akida Alh. Muntari Lawal matsayin wanda zai shugabanci Kwamitin shirya zabukan jam’iyyar.

Rahoto
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
19, July 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here