AN SAKO ‘YAN BATSARI, BAYAN KWANAKI 66 A DAJI .

0

AN SAKO ‘YAN BATSARI, BAYAN KWANAKI 66 A DAJI .
Daga misbahu batsari
A yau juma’a 23-07-2021 aka sako wasu daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka dauka a Batsari.
Idan ba’a manta ba, watanni biyu da doriya da suka gabata ‘yan bindiga masu satar shanu da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, suka dirar ma wasu unguwannin Batsari, inda suka kashe mutum daya, sannan suka sace mutane 28 da tarin dabbobi.
A yau jumma a Allah yayi fitowar
Wasu daga cikinsu.
Zantawar mu da mutanen da aka sako sun bayyana mana irin bakar azabar da suka sha ta yunwa da sauran kuncin rayuwa a zaman su dajin, inda har wani yaron goye ya rasa ransa.
An biya zunzurutun kudi kudi har naira miliyan biyu da rabi N2.5m da zimmar karbo matar Umar Tukur mai suna Hussaina da jinjirinta Al-ameen, sai suka karo masu da mutum hudu, sukace ga barka da sallah nan kamar yadda suka labarta mana.
Ga jerin sunayen mutanen da aka sako:
1. Hussaina Umar.
2. Al-ameen Umar.
3. Marwanatu Bello.
4. Zainab Bello.
5. Muhammad Bello.
6. Yakubu Bello.
Yanzu mutum ashirin da biyu ke hannun masu garkuwa da mutane.
Daga
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here