AbdulJabbar Kabara : Gwamna Ganduje Ya Sha Alwashin Bin Diddigin Lamarin Har Karshe

0
164

AbdulJabbar Kabara : Gwamna Ganduje Ya Sha Alwashin Bin Diddigin Lamarin Har Karshe

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin bin diddigin al’amarin AbdulJabbar Sheikh Nasuru Kabara har zuwa karshensa, tare da tabbacin cewar “…babu shakka wannan yaki ne namu duka gaba daya.”

Ya yi wannan alwashin ne lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga Halifan Darikar Qadiriyyah, Sheikh Qariballah Sheikh Nasiru Kabara, a Gidan Qadiriyyah da ke Kabara, a Kano, ranar Juma’a da tawagarsa.

Ya karfafi gwuiwar Halifan Qadiriyyah da cewa “Kuma mu na gode muku domin kun taka rawar gani. Babu shakka wannan Muqabala wacce a ka shirya, Malamai sun yi aikin nasu na malanta.”

Gwamnan ya ci gaba da cewa “Kuma sun nuna cewar su masana ne. Kuma ba sani kawai ba, su na aiki da sanin. Domin shi ilimi amfaninsa a yi aiki da shi. Akwai masu ilimi amma ba sa aiki da ilimi. Shi ya sa ma mu ka samu kan mu a irin wannan shakiyancin.”

Ya kara tabbatar da cewa “To amma Alhamdulillah an dauko turba yanzu. Idan Allah Ya yarda, gwamnatin Kano za ta ci gaba da bibiya har sai an ga karshen wannan al’amari.”

Tun da farko Gwamna cewa ya yi, ga Halifa Qariballah, “Na ji bayaninka a kan al’amurran da su ka taso na kare Shugabanmu, Shugaban talikai, Annabinmu, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam. Babu shakka wannan yaki namu ne gaba daya.”

A nasa jawabin Qariballah godiya ya yi da cewa “Ina yi wa Maigirma Gwamna maraba da zuwa wannan gida nasa kuma a wannan laburare mai dogon tarihi.”

“Ina so na yi wa Maigirma Gwamna wata jinjina da godiya bisa yadda ya dauki tuta ta kare Mutunci da Alfarma ta Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam a wannan yanayi da wannan lokaci,” in ji Sheikh Qariballah.

Ya sake cewa “Mu na jinjina maka kwarai kuma mu na kara ce maka Allah Ya saka da alheri.”

Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here