JAN HANKALI GA DAKTA MUSTAFA INUWA SAKATAREN GWAMNATIN KATSINA.

0

JAN HANKALI GA DAKTA MUSTAFA INUWA SAKATAREN GWAMNATIN KATSINA.

Daga Kabiru Sadiq

Campaign Council Committee na Gwamna Masari da Muhammadu Buhari a zaben 2019 na Katsina.

An zabo mutane masu muhimmanchi da mutunci da gogewa ta fannoni daban-daban aka sanya su a wannan kwamiti domin ganin an samu nasara a zabukan 2019.

Cikin wannan kwamiti akwai wadanda sama da shekara arba’in da suka gabata sanatoci ne da ‘yan majalisar wakilai ta kasa.

Akwai wanda kusan shekaru arba:in da suka gabata gwamna ne a cikin jihohin Nijeriya, akwar tsofaffin janar na sojan Nijeriya, akwai tsofaffin ‘yan takarar gwamna, akwai manyan malamai na addini, akwai tsofaffin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya da na jiha, akwai manyan yan jam’iyyar mu ta APC da komishinonin gwamnati akwai manyan ‘yan kasuwa da kanana, likitochi, lauyoyi kai duk wani fanni na rayuwar mu to akwai wadanda suka yi fice akai acikin wannan kwamiti.

Mun kai mu 168 a cikin wannan kwamiti kodayake daga baya an kara wasu mutane a ciki.

Wannan kwamiti namu yana karkashin jagoranchin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina dakta Mustafa Inuwa.

An baiwa gwamna tsare tsare na tafiyar da wannan kwamiti ciki harda kudaden da za a rika baiwa mambobi duk lokacin da a ka yi zama.

Saboda wasu suna zuwa ne daga Abuja, Kaduna da Kano wasu kuma daga kananan hukumomin Katsina daban-daban, wannan kudade a kalla zasu iya amfani dasu wajen shan mai, masauki da sauransu.

Wasu kuma a nan cikin gidan gwamnatin zasu rabar da kudin ga jami’an tsaron wurin da sauran kananan ma’aikata.
wasu kuma saboda halin rayuwa manyan mutane ne amma sun dade da ajiye aiki suna bukatar kudin nan domin hidimarsu ta yau da kullum.

BILLAHILLAZI LA ILAHA ILLAHUWA wadannan kudade kashi sittin zuwa saba’in na members ba a basu wadannan kudade ba.
Alhali kuwa duk sadda za a yi zama sai gwamna ya bada wadannan kudade akalla anyi zama 13 zuwa 14.

Kwana goma da suka gabata na zauna da Mustafa Inuwa a gidansa inda na jaddada masa cewar duk wata matsala da yake gani shi ya saye ta da kansa.

Na.gaya masa cikin shekaru shidda bai taimaki ko gina rayuwar kowa ba.
Na bashi misali da hakkin mutane da aka danne a kwamitin yakin neman zabe kalkashin shugabancin sa.

See also  FG APPROVES TRAINING OF 50,000 NON- GRADUATE N-POWER BENEFICIARIES

Ya.bani amsa kamar haka: cewar yana taimakon mutane sosai.
yace wani mutum wanda bai sani ba yayi masa waya ya taimaka masa masan gidansa ya cike,ba inda zai rika shiga, iyalinsa makwabta suke shiga idan bukata ta kama su, yace,ya tura Audu yaje ya duba kuma ya gyara musu masan.
Nace masa ba irin wannan taimakon nake magana ba, taimako na gina rayuwar mutum ya zama mai dogaro da kansa nake nufi.

Akan kudin kwamitin yakin neman zabe Dana yi masa tambaya sai ya bani amsa kamar haka:
Yace abin yana bashi mamaki mutane masu arziki su tsaya suna maganar dubu dari biyu na alawus. Inda yabani labarin akwai sadda Janaral Maharazu Tsiga yayi mashi maganar wadannan kudade, yace Rahusa ma ya taba yi masa maganar, me yasa shi ba a bashi alawus dinshi ba, hakan ma Alhaji Abba Yusuf ma yayi masa magana Kan wadannan kudin a inda yace. Alhaji Abba Yusuf shi ke da Makera Motel kuma wai gwamnati na sauke bakinta a Hotel dinsa yana da arziki amma yazo yana maganar dubu dari biyu,? Inji Mustafa inuwa.
Ni kuma nace masa ko Dangote aka baka kudinsa ka bashi kaki bashi to sai yaji haushi.

Amma shi wai madogararsa wai don suna da arziki ne basu samu alawus dinsu ba.

To shi Mustafa da kanshi ya bani labarin mutum ukku wadanda aka ki ba kudin alawus har ta kai sun yi masa magana, to kashi 60 zuwa 70 ba a basu wadannan kudade ba, har aka gama sabgar nan.

Tambaya ta farko shin wadannan mutane masu muhimmanci a siyasar Katsina zasu goyi bayan Mustafa ya zama Gwamnan Katsina kuwa?

Tambaya ta biyu shin mutumin da aka bashi shugabancin mutanen da basu kai 200 ba, amma suka kasa samun hakkinsu daga wajensa. kuma mutanen nan akwai Janar na soja cikinsu, akwai manyan ‘yan kasuwa masu arziki, ta ina talakkawa milyan kusan goma zasu iya samun fitowar hakkokinsu a kalkashin mulkinsa?

Alhaji kabiru sadiq Dan kasuwa ne kuma dan siyasa mun dauko rubutun ne daga shafin sa na Facebook da ya dora.

@ katsina city news
www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08137777245
Email katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here