AN KAMA MUTANE BIYAR DA AKE ZARGI DA YIN FASIKANCI DA WANI YARO DAN SHEKARA 17 A KATSINA.

0
254

AN KAMA MUTANE BIYAR DA AKE ZARGI DA YIN FASIKANCI DA WANI YARO DAN SHEKARA 17 A KATSINA.
Daga misbahu Ahmad batsari
@katsina city news
A ranar talata 27-07-2021, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tayi nasarar cafke wani kasurgumin dan luwadi wanda yayi amfani da wani yaro dan shekaru goma sha bakwai (17years old). Mutanen da ake zargi da yin lalata da wannan yaro sune; Ibrahim Amadu dan shekaru 42 wanda yake zaune a sabuwar unguwa Katsina, Saminu Abdullahi mai shekaru 25 wanda ke zaune a unguwar Farin yaro Katsina, Jamilu Ibrahim mai shekaru 50 wanda yake zaune a unguwar Farin yaro Katsina, Bashir Lawal mai shekaru 30 yana zaune a gangaren tudun yan lihidda Katsina, sai Mohammed Sani mai shekaru 30 yana zaune a u guwar Saulawa Katsina.
Yaron ya bayyana cewa wata rana wani mai suna Ibrahim Amadu ya dauke shi zuwa wani wuri a cikin garin Katsina, inda ya razana shi wuka kuma ya daure hannuwan shi da igiya, sannan lalata da shi, yace sauran mutanen da aka zayyana ma duk sun aikata masa abinda na farkon yayi masa. Haka kuma ya bayyana karin wasu mutane shida da yace suma sunyi badala da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here