AN KAMA WATA MATA MAI SAFARAR MAKAMAI DA MAKUDDAN KUDI A BATSARI.

0

AN KAMA WATA MATA MAI SAFARAR MAKAMAI DA MAKUDDAN KUDI A BATSARI.

A ranar litanin 19-07-2021 da misalin 09:00am aka kama wata bafulatana mai suna Aisha Nura,

wacce ‘yar kauyen Baranda (Rugar Fulani) ce dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina, matar mai kimanin shekaru 27 an kama ta da tsabar kudi har naira miliyan biyu da dubu dari hudu da biyar, (N2,405,000). Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bakin mai magana da yawunta SP Isah Gambo ya bayyana cewa sunyi nasarar kama matar ne sakamakon bayanan sirri da suka samu, inda suka cafke ta a cikin garin Batsari ta jihar Katsina, lokacin da take neman dan acaba da zai kai ta kauyen Nahuta. Da aka bincike ta ne aka same ta da wadannan kudi wanda ake tsammanin tana safarar makamai ne ga ‘yan bindiga na yankin jihar Kaduna.
Daga karshe ta bayyana ma rundunar ‘yan sanda cewa, ita matar wani dan bindiga ce mai suna Nura Alhaji Murnai wanda yake karkashin dabar Abu Radda, kuma shine(Radda) ya tura ta dajin Kaduna domin ta karbo masa kudin wuri abukkan huddar su dake can.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here