MUSA HARO YA ZAMA HAKIMIN DUMURKUL.

0

MUSA HARO YA ZAMA HAKIMIN DUMURKUL.
muazu hassan
@ katsina city news
Mai Martaba sarkin Daura dakta Umar Farouk Umar ya ba Alhaji Musa haro sarautar hakimin sabuwar masarautar dumurkul.
Alhaji Musa haro a yanzu yana rike da matsayin Dan madamin daura .
Sanarwar tana a wata takarda da masarautar Daura ta aika ma Alhaji musa haro wadda jaridun katsina city news suka samu kwafi.
A takardar an zayyana garuruwan da zasu kasance a cikin gudummuwar dumurkul sabuwa.
Garuruwan sun hada da dumurkul.jirdede.kokutoko ,bula,kakalgon dangwara.yikka.mammani,,Raba,gagir,jassai, yan Hakum,tilla da sukuf.
Ita dai sabuwar masarautar dumurkul itace ainihin inda aka Haifi shugaban kasa Muhammad Buhari.
Sunan ta ya fara fitowa a wani rubutun daily trust a watan Maris na 2019.
Sunan garin ya fantsama har ya kai ga samun hakimanci daga rubutun da mujallun katsina city news suka kara bugawa akan garin a fitowar ta watan March 2021.
Katsina city news @ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here