RIKICI A PDP KATSINA; MAJIGIRI DA LADO SUN SA ZARE

0

RIKICI A PDP KATSINA;
MAJIGIRI DA LADO SUN SA ZARE

Misbahu Ahmad
@ Katsina City News

Wani mummunan rikici yana ruruwa a tsakanin Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Katsina da mutanensa da kuma Alhaji Yakubu Lado Dan Marke, dan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP a zaben 2019, kamar yadda jaridun Katsina City News suka bincika, kuma suka tabbatar.

Binciken da jaridar nan ta yi ta gano dalilai da yawa da suka haddasa fitinar, kuma take ruruwa da yaduwa a cikin babbar jam’iyyar adawar da ta yi shekaru 16 tana mulkin Katsina.

Bincikenmu ya gano wani kokari da bangaren Majigiri ke yi na dinke jam’iyyar waje guda da janye duk wasu shari’u da ke a gaban kotu. Wannan shi ne kashin bayan rikicin.

Bincikenmu ya tabbatar mana bangaren Majigiri sun dau lokaci suna zaman tattaunawa da bangaren ‘yan PDP a-gyara, wadanda suka samo hukuncin kotu na rusa shugabancin su Majigiri a Jiha, shari’ar da yanzu haka taken gaban kotun daukaka kara da ke Kaduna.

Bayan zama na watanni kamar yadda muka tabbatar, daga karshe an cimma wata matsaya ta a bai wa bangaren PDP a-gyara mukamai da suka nema a Kananan Hukumomi 21, su kuma su janye duk kararrakin da suka shigar a zama a lema daya.

Wannan tsari shi ne Yakubu Lado ya sa kafa ya yi fatali da shi, tare da jin cewa an ci amanarsa. Don haka wasu ke zargin ya sha alwashin sai yaki su Majigiri da Shema a jam’iyyar PDP.

Katsina City News ta saurari wata murya da aka nada a waya, wadda ake zargin ta Yakubu Lado ce, a ciki an ji mai maganar yana bayyana yadda ya rika daukar dawainiya da hidimomin jam’iyyar PDP da manyanta a Jihar Katsina tun daga 2019 har yanzu, amma an zo za a ci masa amana.

A muryar an ji mai maganar yana shan alwashin sai ya ga kwal uwar daka.

Wannan tsari na ba PDP a-gyara wasu Kananan Hukumomi don a daidaita a zama daya shi ne ake zargin Lado yake gani a matsayin barazana a aniyarsa ta zama Gwamna.

Wani na kusa da Lado din ya bayyana mamakinsa a kan yadda za a mika Kananan Hukumomi 21 ga makiyansa.

Bincikenmu da tattaunawar da muka yi da bangaren PDP a-gyara da kuma na Majigiri sun tabbatar mana akwai wancan shirin na daidaitawa don a zama daya.

Wata majiya mai tushe ta shaida mana cewa wani dalili da ya sa PDP bangaren Shema, wanda Majigiri ke ciki, suka tattauna da yanke shawarar cewa a zaben 2023, PDP za ta tsayar da dan takara na kwarai mai abin da za a tallata shi da su. “Duk abin da suka zayyana Yakubu Lado bai da ko daya. Don haka tun yanzu muka fara nesa-nesa da shi”, in ji majiyar tamu.

See also  DAN TAKARAR GWAMNA A JAM'IYYAR APC ZAI GINA KASUWAR ZAMANI A KARAMAR HUKUMAR BAKORI.

Ko a muryar da muka ji da ake zargin ta Lado ce, akwai inda yake cewa: “Tun ba a je ko’ina ba har an fara yi mani makirci da cin amana a kan takara ta a 2023”.

Bincikenmu ya gano a zaben shugabannin PDP na wannan shiyyar, wanda aka yi a Kaduna, a nan barakar Lado da Majigiri ta fara fitowa, inda Shugaban na PDP ya goyi bayan ‘yan takarar Tambuwal, yayin da shi kuma tsohon dan takarar Gwamna ya goyi bayan ‘yan takarar Kwankwaso.

A nan ma an ruwaito wai Yakubu Lado yana yada ‘yan maganganu da wasu zarge-zarge marasa tabbas.

Bincikenmu ya gano Yakubu Lado yana ta tarurruka da kungiyoyi da jiga-jigan jam’iyyar PDP a Katsina domin samar wa kansa madafa.

Ya ruwaito shi yana shan alwashin in har kudi ke yi, to lallai zai kara da kowa a PDP kwabo da kwabo.

Mun samu tabbacin ya gana da wasu tsaffin ‘yan takarkari a jam’iyyar da kuma wasu jiga-jigai.

An kuma ruwaito yana cewa zai tare Katsina da zama don yakar su Shema da Majigiri a jam’iyyar PDP.

Wannan rikicin ya fantsama hatta a tsakanin wasu manyan jam’iyyar inda suka dau bangare, yayin da Shema, Majigiri, Sanata Tsauri ke bangare daya, su kuwa wasu tsaffin ‘yan Majalisun Tarayya biyu da wasu masu rike da mukamai a Jiha suna bangaren Lado.

Bincikenmu ya gano wasu sun tsaya tsaka tsaki suna ta ban baki a tsakani, irin su Alhaji Mustafa Musa ‘Yar’adua.

Mun yi kokarin jin ta bakin Alhaji Salisu Yusufu Majigiri hakarmu ba ta cimma ruwa ba. Mun kira bai dauki wayarmu ba, shi ma Yakubu Lado Dan Marke haka, kuma bai dawo mana da sakon waya da muka aika masa ba.

Rikicin yin abin da ya dace da kuma na son rai na shirin fasa jam’iyyar ta PDP kafin zaben 2023 a Katsina.
Duk yan PDP a gyara da jaridun sukayi magana dasu sun mika wuya don ayi sulhu,haka PDP bangaren majigiri, amma Yakubu lado da mutanen sa,sun sha alwashin sai sunga abin da ya ture ma buzu nadi.!!

Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here