SHARI’O’IN IBRAHIM SHEMA SUN DAUKI SABON SALO
_*AN CIRE MAKANA DA SAFANA_
_*AN DAUKE ALKALIYAR KOTU_
@Katsina City News
Shari’o’i guda biyu da ke gaban manyan kotuna a Katsina da ake yi tsakanin Hukumar EFCC da kuma tsohon Gwamnan Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, sun dauki sabon salo.
Shari’a ta farko da ake yi a babbar kotun Jihar Katsina a kan kudaden Kananan Hukumomi, wadda ta kai matsayin gab da kammala kawo shaidu, sai Allah ya yi wa Alkalin rasuwa.
Da aka canza mata Alkali, aka sake sabon zama, wadda za ta fara daga farko ke nan.
Sai Hukumar EFCC suka fitar da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Alhaji Sani Makana, wanda ake tuhuma na uku da kuma Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomin Katsina ta lokacin, Alhaji Lawal Rufa’i Safana, wanda ake tuhuma na hudu.
A zaman farko Lauyan EFCC ya bayyana cewa suna bukatar a fitar da su biyun ne domin bincikensu ya tabbatar masu da cewa ba inda suka aikata ba daidai ba. Don haka ba su da laifin da za su tsaya a gaban shari’a don a tabbatar da shi. A haka aka dage zuwa zama na gaba.
A zaman da kotun ta yi karshen watan Yuli da ya gabata, Alkalin ya amince da bukatar Lauyan EFCC masu shigar da kara.
A wannan zaman aka fitar da su Lawal Rufa’i Safana da Sani Hamisu Makana daga zargin aikata ba daidai ba, kuma aka sallame su.
A ranar aka sake sabuwar tuhuma da karanta wa wanda ake zargi na farko da kuma na biyu; Alhaji Ibrahim Shema da kuma Alhaji Ibrahim Lawal Dankaba.
Bayan karanta masu tuhume-tuhumen an daga shari’ar ar zuwa tsakiyar watan Satumba 2021.
Wata majiya a Hukumar EFCC ta ce tun farkon binciken a 2015 zuwa 2016, Lauyoyin EFCC suka ba gwamnatin Katsina shawara a kan kar a saka Lawal Rufa’i Safana cikin tuhumar, saboda duk wata ka’ida ta aiki sai da ya cika ta a takardun da ke gabansu, amma ana zargin wani mai fada aji a gwamnatin Katsina ne ya dage sai an makala shi. Bayan shekaru yanzu kuma an dawo an cire shi.
A shari’ar da ake yi a babbar Kotun Tarayya da ke Katsina, ita ma Hukumar EFCC na gab da kammala ba da shaidu, sai aka dauke Alkaliyar zuwa Kaduna.
Hukumar EFCC na neman a ci gaba da shari’ar a Katsina, wacce za ta koma sabuwa fil ke nan, su kuma Lauyoyin Shema na neman a ci gaba a Kaduna tun da ta kusa zuwa karshe, saura shaidu biyu kacal suka rage a saurari jawabin Lauyoyi da yanke hukunci.
Ana sauraren inda za ta kaya. Karasa ta za a yi a Katsina, ko fara ta sabuwa a Kaduna?
@Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com
07043777779.08137777246
katsinaoffice@yahoo.com