BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA TSOHON GWAMNAN JIHAR KATSINA, BARR. IBRAHIM SHEHU SHEMA [2007-2015].

0

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA TSOHON GWAMNAN JIHAR KATSINA, BARR. IBRAHIM SHEHU SHEMA [2007-2015].

Daga Yasir Ibrahim

Assalamu Alaikum!

Ranka ya dade, da fatan ka wuni lafia.

Cikin fatan alkhairi akoda yaushe, ranka ya dade, ina mai matukar farinciki da rashin yin da nasanin yimaka albishir cewa – ” Mutanen Katsina nata godiya da mararin gwamnatinka bisa irin aiki na azo a gani da tayi ba ashararanci ba. ”

Tabbas, a tsawon mulkinka da fadi tashi da kaitayi wajen ganin ka inganta jihar Katsina. Mu al’ummar Katsina bamu da kamar ka kuma baza mu taba iya biyanka sai sai fatan alkairi gareka.

Ranka ya dade Kayima Allah godiya daya dauko ka ya sanya ka zama misali kuma abun koyi ga duk wani shugaba ko matashi mai hangen nesa, dabara da sanin makamar aiki. Yanzu kusan shekara bakwai kenan da gama shuwagancinka, amma zamu iya cewa, aiyukan da kayi a fanni daban daban daya shafi bangaren ilimi kyauta, kiwon lafiya, hanyoyi masu inganci da gine gine na cigaban al’umma, ruwa da tsaftace muhalli da kuma gina mutane da aikinyi, sana’oi da kwarewa ta sanin makamar aiki sunanan al’umma nata amfana dasu. Wanda zamu iya cewa da basu Allah kadai yasan yadda Katsina zata koma kawowa yanzu.

Kowa yasani cewa Gwamna Shema dan kishin jihar Katsina ne kuma mai son cigabanta. Bayan ya kammala shekara takwas dinshi a matsayin Gwamnan Jihar, sanin kowa ne yaso Katsina ta koma hannu na gari, hannun mutum mai tausayi da sanin makamar aiki. Domin hakanne kawai zai bada damar idashe ayyukansa na alkhairi a jihar Katsina. Amma in kuma muka kalli wannan gwamnati ta yan bakinciki, hassada, tunzura talaka da nuna kowa bai iyaba sai su, zamu ga cewa babu abunda sukayi inba maida jahar Katsina matalauciya da zama koma baya ba. Gwamnatin Masari ba tayi wani aiki da har za’a kalla a hada dana Gwamnan Gwamnoni Ibrahim Shema ba.

Sanin kowa ne PDP ta jihar Katsina tana fuskantar rashin jituwa tsakanin bangarori biyu da take dasu. Ranka Ya dade, Allah ya azurtaka ya kuma baka daukaka a kasarnan baki daya, bawai Jihar Katsina kadai ba. Lokacin da kayi Gwamnan Jihar Katsina, sanin kowa ne ka tabbatar ma duniya kai shugaba ne mai kwarjini, mai bada horo da da’a wanda ya zamo abun koyi ga shugabancin Afrika gabaki daya. Har kagama mulkinka jam’iyar PDP a Katsina bamu taba samun rabuwar kaiba ko hatsaniya irin wannan ba.

Ranka ya dade, ayi hakuri da wannan maganar da zan fadi ” Wannan rabuwar kawuna da ake samu a jam’iyar PDP, tasamo asali ne saboda ja bayan da kayi da nuna ko in kula da kakeyi a hidimar jam’iya.”

Dalili na cewa haka kuwa baya wuce:

Ranka ya dade, ina da tabbacin cewa, duka wainnan bangarori biyu sun amince kaine jagoransu kuma suna baka girmanka akoda yaushe.

Wannan lokaci ne da yakamata mu cire wani boyayyen ra’ayi a gefe muzo muyi abunda zai kawo cigaba a jam’iyyar PDP da kasa baki daya. Jihar Katsina, fiye da ko yaushe, tana bukatar kwarewarka da jagorancinka domin fita daga wannan hali na tabarbarewa da lalacewa da take ciki. Ranka ya dade, Katsina na neman daukin ka domin koma wa akan turbar da kai da Maragayi Umaru Musa kuka ginata akai. Sanin kowa ne, yanzu Katsina na cikin tsananin talauci daya samo asali saboda rashawa da lalata dukiyar jaha da shuwagabannin mu keyi ba dare ba rana. Zabar yan dagaji amatsayin shugabanni masu kula da offisosun gwamnati ya zama ruwan dare awannan gwamnati. Yunwa tayi yawa, ba aikinyi. Rashin tsaro yakai lalacewar da wasu garurrukan ma a hannun yan ta’adda suke, daruruwan mutane sunyi hijira sun bar garuruwansu, noma ya gagari talaka. Asibiti ba magani, gine gine nata rushewa saboda ba kula. Ilimi yazama sai dan wane da wane.

Matsayinka na jagora kuma uban jam’iya a jihar Katsina baki daya. Inaga ya kamata ka shirya zama da jagorori na wannan bangarori domin shirya kawunansu, shirya kawunan su din zaiyi tasiri sosai wajen kawo karshen wannan koma baya da jam’iyar PDP ke fuskanta. Rashin yin hakan kuwa zai iya jawo wasu bangarorin su kara samu cikin Wani halin da komabaya Wanda zaisa muki samun nasara zabe Mai zuwa.

Daga karshe ina kiran ga mai girma Gwamna Shema da babbar murya da yayi amfani da basira, ilimi da iya shugabanci da Alkalanci da Allah ya azurtashi dashi ya zabo mana mutum ingantacce bawai mai tarin dukiya ba farin jini ba. Ya kuma samo matsashi mai hazaka da kaifin basira a matsayin mataimakinshi. Hakan zai baiwa PDP dama tayi saukin saidawa ga al’ummar Jahar Katsina. Ta kuma yi mulki mai tsabta da zai kawo cigaba mai dorewa, zaman lafia, hadin kai da adalci.

In muka dauki zabe na shekarar 2015, a wannan lokacin PDP itace akan karagar mulki, tana da kudi masu suna kudi da zata iya amfani dasu taci mulki da kuri’oi masu yawa, amma sai gashi kudin basuyi rana ba.

Babu abunda PDP tafi bukata a yanzu face jagora wanda zai zama abun bada misali ga al’ummar jihar katsina. Ranka ya dade, kowa yasan irin aiyukan da kayi a kowane bangare na jihar Katsina. A zaben 2015 mutane basu fahimci hikimarka ta kawo Ibrahim Na Shuni ba, amma zan iya cewa yanzu sun ankare sun kuma yi hankali.

Kowa yasan cewa jam’iyar adawa tana bukatar kudi masu yawa domin cin zabe. Sir, kai kwararre ne a bangaren siyasa kuma malami akan dabarun cin zabe. Inaga ko bamu tsaida mai kudi ba in har za’a samu hadin kai ta hanyar tsaida wanda ya cancanta bawai al’farma ba, jam’iya zata iya samun kudade ta hanyoyi da dama da zasu iya kaita ga cin zabe.

Saboda a PDP ta jihar Katsina akwai masu neman wannan kujerar da dama wanda inhar ba’a zauna anyi sasanci an zabi wanda ya cancanta ba, daga karshe zasu iya yima jam’iyar gwamnati aiki domin huce takaicinsu.

Ranka ya dade, inama addu’a Allah ya karama nisan kwana, lafia da daukaka. Ina kuma fatan wannnan budadden sako nawa zai isar maka, zai kuma zama salar kawo karshen wannan matsala da jam’iyar PDP ke fuskanta.

Nagode.

*Yasir Ibrahim*
*Dan Gwagwarmaya.*
*Dan Cikin Garin Katsina*
*Wakilin Kudu 111*

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here