DA RANA KATA ‘YAN BINDIGA SUKA KAI HARI BATSARI.
YAN BINDIGA SUN KAI HARI DA RANA A GARIN BATSARI
misbahu Ahmada
@ katsina city news
Da yammacin talata 03-08-2021 ‘yan bindiga suka kai hari Batsari ta jihar Katsina da Rana kata.
Wasu mahara kan babura dauke da miyagun makamai sun kai hari unguwar tafkin kura dake yammacin Batsari, inda suka harbi mutum biyu daya ya rasu daya kuma yana asibita yana karbar magani.
Wani da ya gane ma idanun shi yace yana gona yana aiki sai ya ga babaura gudu hudu dauke da mutum biyu-biyu, suka wuce shi suka nufi bakin gari inda suka yita harbi kan mai uwa da wabi.
Koda yake inda suka kai harin yayi wajen gari , amma duk da haka sun kidima mutane sosai inda mata da kananan yara suka kama gudun tsira.
A satin da ya gabata rana irin ta yau, sun kawo irin wannan harin wanda suka harbi wani mai suna surajo a kafa, yanzu haka yana nan yana jinya. Wasu da suka nemi mu sakaya sunansu sun bayyana mana cewa wannan hare-haren bai rasa nasaba da kama masu wata mata mai suna Aisha Nura wadda aka kama da makuddan kudi da suka haura naira miliyan biyu, ance sun nemi a sake ta ko kuma su dauki mataki
Katsina city news
@ katsinaoffice@yahoo.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
070 43777779 08137777245