NA RANTSE DA ALLAH; BA ZANCI AMANAR PDP BA.
….INJI MAJIGIRI
@ katsina city news
Shugaban jam iyyar PDP ta jahar katsina,Alhaji salisu Yusufu majigiri ya yi rantsuwa da Allah cewa ba zai taba cin amanar jam iyyar PDP ba.
” Da inci amanar jam iyyar PDP gara in bar wannan kujerar ta shugaba da nake a bisa” inji shi
Majigiri yana magana a taron shugabannin jam iyyar PDP da suka taru a ofishin jam iyyar dake titin hanyar Kano a ranar larabar data gabata.
Daga cikin shugabannin da suka hadu akwai ciyamomin kananan hukumomin guda 32.da yan kwamitin zartarwa guda ashirin. Da duk zababbun masu mukamai.banda marigayi Alhaji bashir sada tsanni.wanda Allah yayi ma rasuwa.
A taron majigiri yace baya da ikon daukar kujerar kowa ya ba wani .balle har kujeru sama da ashirin.
Yace tabbas, ana tattaunawa da wasu yan jam iyyar da ransu ya baci.amma duk a tattaunawar babu inda za a taba yarda aci amanar jam iyya.ko ya yanta.
Bayan gama dogon bayanin shi , shugabannin jam iyyar na kananan hukumomi daban daban suka yi jawabin jaddada goyon baya ga majigiri da shugabannin jam iyyar.
Kuma aka zartar da amincewa duk shugabannin jam iyyar tun daga kananan hukumomi zuwa jaha zasu hadu suyi a lema daya suyi aiki tare don cigaban jam iyyar.
Har aka kammala taron ba ambaci sunan kowa ba,Wanda ake wata ja in ja dashi.ko wasu da ake da matsala dasu.
Daga karshe anyi maganar rijistar yan jam iyyar PDP da za a fara daga ranar litinin mai zuwa .
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245