FITAR DA GWAMNA A APC; FUNTUA CE RABA GARDAMA

0

FITAR DA GWAMNA A APC; FUNTUA CE RABA GARDAMA

Mu’azu Hassan
@ Katsina City News

Siyasa da takara ‘yan lissafi ne. Makonni biyu da suka wuce aka yi zaben shugabannin unguwani na jam’iyyar APC.

A jiya Asabar kwamitin da aka turo daga Abuja ya ba Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari rahoton wucin gadi na sakamakon zaben.

A zaben fitar da ‘yan takarar na mazabu, yanzu an gama mai wahala, sauran kamar karasawa ne.

Duk wanda da ke niyyar takara ya yi kokarin ganin ya samu shugabanni a unguwani da yawa.

Daga bincikenmu, wanda muka tabbatar ta bayanan da muka tattara da rahoton da ‘yan kwamitin da suka zo daga Abuja muka leko shi ta barauniyar hanya.

Duk ‘yan takarar da ke da wakilai a kwamitin shirya zaben shugabannin, babu wanda ya samu Kananan Hukumomi shida da yake iko da su 70% din. Babu sam-sam. Kowa ya rika dibar wani abu a kwace unguwa ne. Wani ya samu 50, a wani wurin ya samu 30 ya hakura. Muna da cikakken nazarin karfin kowane mai neman takara a kowace Karamar Hukuma.

A lissafin da ake da shi a yanzu in yanzu za a tafi zaben na fitar da dan takara, yankin Funtua ne zai raba gardama. Domin a yankin ne wani dan siyasa guda daya wanda ba zai takara ba a saninmu, zuwa yanzu yake da Kananan Hukumomi bakwai cif a hannunsa, yana da kashi 80% na ‘yan wadannan Kananan Hukumomin bakwai cif. Sauran Kananan Hukumomin, wasu yana da 40, wasu kuma 50.

See also  YAU SHUGABAN KASA BUHARI ZAI TAYA GWAMNAN KATSINA MASARI MURNAR NASARAR DA YA SAMU A KOTU

Yankin Funtua ne, wanda in yanzu aka shiga zaben fitar da dan takara in suka zo da murya daya za su raba gardama fitar da wanda jam’iyyar APC za ta tsayar.

A yankunan Daura da Katsina, abin da bincikenmu ya tabbatar mana babu wani dan takara daya da zai iya bugun gaban yana da ita.

In wani ya yi sama a wani wuri, sai kuma ya yi kasa a wani bangaren.

A zaben fitar da dan takara (Deliget) maciya amana ne, ba su da tabbas.

Marigayi Kanti Bello ya taba misalta su da sun fi ‘yan Boko Haram bala’i, amma dole a lissafi ka lissafa da abin da kake da su. Wannan shi ne lissafin yanzu, ba wanda ya san ya gobe za ta yi sai Allah.

@ Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
www.thelinksnews.com
070 43777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here