KVC ZA TA YI BUKIN RANAR MATASA TA DUNIYA RAN 12 GA AGUSTA

0

KVC ZA TA YI BUKIN RANAR MATASA TA DUNIYA RAN 12 GA AGUSTA
.
Shaharariyyar cibiyar nan da Marigayi Alhaji MD Yusufu, tsohon Sufeto-janar na ‘yan sanda a shekarar 1976 zuwa 1979, mai suna KATSINA VOCATIONAL TRAINING CENTRE, ya kafa a shekarar 2001 don horas da matasa sana’o’i da kuma farkar da zukatansu, za ta gudanar da taron ranar matasa ta duniya a ranar Alhamis 12 ga watan Agusta da kuma yaye daliban da ta horas.

Cibiyar, wadda daga kafa ta, ta horas da dubban matasa, za ta hada bukin da kuma yaye wasu daliban da ta horas a tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021.

Bukin zai hada da ba da kayan sana’a da kuma jari ga wadanda suka cancanta da lakcoci.

Wannan bukin shi ne na 19 da kafuwar Cibiyar a shekaru 20.

A baya fitattun mutane sun halarci taron da Cibiyar ta shirya, inda suka gabatar da jawabin da ya zama alkibla da kuma mafita ga kasar nan.

Daga cikin wadanda suka halarta a baya akwai tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua (Allah ya ji kansa), tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya; Malam Sanusi Lamido Sanusi, tsohon Shugaban Kotun daukaka kara ta kasa; Mai Shari’a Umaru Abdullahi (Walin Hausa), tsohuwar Shugabar Hukumar EFCC; Hajiya Farida Waziri, Farfesa Danjuma Maiwada; tsohon Shugaban Jami’ar Alkalam, tsohon Shugaban Jami’ar Umaru Musa; Farfesa Isah Funtua, Farfesa Sani Abubakar Lugga Wazirin Katsina da sauransu.

Taron na bana zai gudana ne a dakin taro na Sakatariyar Gwamnatin Jihar Katsina, ranar Alhamis 12 ga watan Agusta, 2021 da karfe 10:00 na safe.

Taken taron na bana shi ne gudummuwar da matasa za su bayar a wajen inganta tsaro da kuma tsabtace siyasa a kasarmu.

Kwararru ne za su gabatar da mukala a taron daga cikinsu akwai Farfesa Sanusi Sanusi, Mamman Shugaban Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da Dakta Muttaka Rabe Darma, Dakta Albaba, Dakta Bashir Abu Sabe, Malam Ibrahim Ahmad Katsina, mai ba Gwamnan Katsina shawara a kan harkar tsaro, zai wa jawabin dauraya.

Shugaban taron na bana shi ne Alhaji Lamisi Dikko, Ajiyan Katsina, Hamshakin dan kasuwa, kuma gogaggen dan siyasa.

Babban bako shi ne
Mai Shari’a Umaru
Abdullahi, Walin Hausa.

Babban bako na musamman, mai girma Gwamna Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari CFR,
Dallatun Katsina.

Mai gayyata da gabatar da taron na bana shi ne Alhaji Musa Danladi Abubakar, dan kwamitin amintattun Cibiyar, kuma babban Jojin Jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here