YAN BINDIGA SUN BINDIGE WANDA YAJE KAI KUDIN FANSA A BATSARI.

0

‘YAN BINDIGA SUN BINDIGE WANDA YAJE KAI KUDIN FANSA A BATSARI.
Misbahu Ahmad batsari
@ katsina city news
Da yammacin ranar litinin 09-08-2021 wasu ‘yan bindiga suka harbe wani bawan Allah mai suna Ibrahim Na-karkara, mazaunin unguwar katoge ta karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.
Marigayin ya hadu da ajalinsa ne da misalin karfe tara (9:00pm) na dare akan hanyar shi ta dawowa gida Batsari, bayan ya kai kudin fansa da nufin ‘yanto matar shi da diyar shi wadanda suna cikin mutane 22 ‘yan Batsari da suka dauka cikin garin kimanin kwanaki tamanin da suka gabata.
Lamarin ya faru akan hanyar Ruma zuwa Batsari inda ake zaton wasu ne suka yi kwanton bauna daidai kauyen kabobi, dab da shiga kauyen Gobirawa .
sun bude masa wuta yana bisa babur inda da gari ya waye aka samu gawar shi.
Har zuwa rubuta rahoton nan babu cikakken bayanin me ya faru? Kuma ba a sako matar tashi da Dan sa da ya kai kudin fansar amso su ba.
Su dai mutane ashirin da biyun suna cikin wadanda yan ta adda suka shiga har garin batsari suka tafi dasu daji wata uku da suk wuce.
A kwanakin baya an biya kudi aka sako biyu.kuma yan bindigar suka sako hudu a matsayin goron sallah.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email katsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here