Ranar Matasa Ta Duniya: Mata 50 Sun Samu Tallafi Daga S.A Mai Turaka

0

Ranar Matasa Ta Duniya: Mata 50 Sun Samu Tallafi Daga S.A Mai Turaka

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Mai taimakawa gwamnan jihar Katsina akan wayar da kan jama’a Alhaji Abdul’aziz Mia Turaka ya tallafawa mata da suka samu hore da cibiyar koyar da sana’o’I ta marigayi MD Yusud (Katsina Vocational Center) a wani mataki na kara fadada aikin cibiyar.

Matan sun sami tallafin naira dubu goma kowace daga cikin su domin samun dan abin da za su fara yin sana’a da za su rike kan su da ita, mata hamsin ne suka amfana da wannan tallafi daga bangarorin koyan sana’o’I daban daban a wannan cibiya.

Wannan biki dai yana zuwa ne a ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin tunawa da ranar matasa ta duniya, kuma bikin ya yi daidai kasancewar matasa ne suka samu horan domin samun abinda za su yi dogara da kansu anan gaba.

Jim kadan bayan kammala mika wannan gudunmawa S.A Mai Turaka ya samu zarafin tofa albarkacin bakinsa game da wannan gawurtatccen taro wanda ya hada duk wani mai ruwa da tsaki na jihar Katsina domin ganin abubuwa da za su kasance.

Alhaji Mai Turaka ya nuna farin cikinsa akan wannan taro sannan ya yabawa wadanda suka shirya wannan taro saboda irin kwazo da jajricewar da aka nuna wajan ganin an samu nasara taron kamar yadda aka gani

“Ina kari ga malamanmu da su tashi tsaye wajan ganin sun kara fadakar da iyaye wajan ganin ‘ya ‘yan su sun yi abinda suka dora su akai, domin bijirewa umarnin iyaye ne ya jefa da yawan matasa cikin wahala, saboda haka akwai aikin gaban malamanmu wajan fadakar da iyaye.” In ji shi

See also  FG completes road intervention at FMC,Yenagoa

Mai Turaka ya bayyana cewa mai girma gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari kullin yana horansu da su rika taimakawa masu karamin karfin domi kara ba su kwarin gwiwa wajan tsayuwa da kafafuwansu har su taimaki wasu.

Kazalika ya yaba da irin yadda komi yake tafiya bisa tsari da nuna kamala da dattako musamman daliban wajan gudanar da wannan taro, yana mai kira ga masu hannun da shuni da su rika taimakawa marasa karfi a duk lokacin da bukatar hakan ta ta so.

A karshe dai Mai Turaka ya bayyana cewa wadannan kudi naira dubu dari biyar da ya bada tallafi yna rokon Allah ya amsa ya kuma kai ladar ga mahaifiyarsa wanda suke tare da ita yanzu a wannan rayuwa ta duniya mai cike da darasin rayuwa.

Cibiyar marigayi MD Yusuf (Katsina Votional Center) ta samu nasara horaswa tare da yaye dalibai 315 a wannan shekarar ta 2021 kuma a wannan shekarar ne take cika shekaru ashirin cif da kafuwa.

Wannan taro na bana yana a matsayin wani baban tarihi da cibiyar ta kafa, bayan shafe sheru 20 tana gudanar da irin wannan aikin na jin kai ga al’umma kyauta, ba tare da ko sisi ba, sannan tayi bikin ne a dai dai ranar da matasa ke biki ranar matasa ta duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here