SAKON MASARI DA KOWA YA KARE KANSA ..A TARIHIN YAKI.

0

SAKON MASARI DA KOWA YA KARE KANSA ..A TARIHIN YAKI.

Danjuma Katsina

Ina daya da cikin na kusa da Marigayi MD Yusufu har Allah ya dau ransa.

Ina cikin wadanda yake sa wa aiki na amana. Wata rana ina gyara masa wasu takardu da ya sanya ni. Don yana neman wasu takardun da bai gane ina ya ajiye su ba. Sai ga wani rahoto da ya sanya a buga shi a kuma dinke shi, sama an rubuta “Biafran War; Security and Civil Defence”. Nan take na fada masa ga takardun da yake nema.

Ya dauka ya duba, ya dau waya ya kira Ministan cikin gida na lokacin, Ambasada Magaji Muhammad. Wannan ganawar ce ta haifar da kafa Hukumar tsaro da taimakon gaggawa na Civil Defence.

A lokacin Olusegun Obasanjo yana Shugaban Kasa ya mai da ita doka.

Bisa amincewarsa na karanta wadancan takardun. Labari ne na wani tsari da MD Yusufu. Lamido Sanusi ( mahaifin tsohon sarkin kano na da)da Marigayi Ahmad Joda( Wanda ya rasu kwanan nan) suka tsara kuma suke tafiyarwa.
Tsarin shine .
An samu kabilun da ba su goyon bayan yakin Biafra aka horas da su da kuma tsara masu yadda za su kare kansu da bayar da bayanai ga gwamnatin Nijeriya da kuma bada taimakon gaggawa ga wadanda hatsarin yaki ya rutsa dasu.

Sai kuma Inyamurai da ba su goyon bayan yakin Biafra yadda za su kare kansu, su kai daukin gaggawa ga talakawa in hari ya rutsa da su da kuma yadda za su yi wa sojan Biafra makarkashiya.

Duk shirin baki dayansa ana yi ne da mutane wadanda ba su aikin kowane fannin tsaro ko kaki.

Wannan aiki da aka yi da wadanda suke ba jami’an tsaro ba, shi ne ya rika kawo nasara ga yakin, ba gumurzun fagen dagar soja ba zalla.

Ojukwu ya fadi a rubutunsa da yawa in da yake cewa zagon kasa da yakin cikin gida ya ci shi! ba fadan fagen daga ba.!

A wani jawabin da tsohon shugaban kasa janar Gawon ya yi a shekarar 2013 wajen kaddamar da littafin MD Yusufu a dakin taro na Arewa House, ya ce; “MD Yusufu suka fito da tsarin yadda wadanda ba ruwansu da yakin za su kare kansu. Su raunana abokan gaba, su kuma kai daukin gaggawa ga wadanda hatsarin yaki ya rutsa da su wannan aikin ya rage yawan rasa rayuka da barnar dukiya fiye da farmakin soja”.

A lokacin yakin na Biafra da su MD Yusufu suka ji ba su da aminci dari bisa dari da Inyamurai da ke ba su labarai.

Wasu mutane suka dauko daga wata kasa masu kama da Inyamurai aka ba su horo aka tura su garuruwan Inyamurai.

Ni na San wasu daga cikin wadanda suka yi wannan aikin, dayan su ya fada mani baka da baka, ya ce; “Aikinmu in mun shiga gari shi ne karfafa fararen hula yadda za su kare kansu da taimakon gaggawa ga wadanda hatsarin yaki ya fada wa. Sai kuma makarkashiya ga sojan Biafra” .

Kwamandojin da aka yi yakin Biafra da su sun san irin rawar da mutanen gari suka ba da.wanda duk garin da aka ci sai dai a ba da kariya kawai.
Amma kowane gari suna da tsarin kare kansu da kansu. Ba sa jiran isowar soja.

Duk duniya a yaki, ba sojan fagen daga ke nasara ba, a’a wani kokarin da mutane ke wa kansu da kansu.

Irin haka yake a tarihin yakin duniya na farko da na biyu da wasu yakokin da suka shiga cikin tarihi, inda wasu talakawa ke kafa sojan kare kai da sa kai, don tsira da mutuncinsu.
Ko yakin da aka gama kwanan a kasar Afghanistan,zakaji a labarai ana fadin a Kwashi farar hula da suka taimaki sojan yammacin turai.
A yaki ya
In ka ce sai jami in tsaro ya zo kai ne kullum kake cikin bakin ciki, kuma kai za ta shafa, wanda ke mulkinka da Attajiri,shi sai dai tsautsayi in ya ratsa.

Bambancin wanda gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ke magana da kuma na baya na tarihi,shi ne.

A baya, kamar yadda tarihi ya zo da shi gwamnatoci ne ke tsara shi a tsanake bisa hanya tsararra, ilmi da hankali na aiki, amma in aka bar abin zubar-gada za a samu ta’addaci da rashin imani daga kowane bangare, wani ya yi cikin fushi, wani kuma don daukar fansa.
Tarihi ya kawo jama’a su kare kansu, amma bisa ilmi da tsari, kuma duk al’ummar da suka dogara da cewa sai jami’an tsaro kawai za su kare su, suna cikin ganin bone.
Gwamnatin Jihar Katsina ta damu da matsalar tsaro, kuma tana kashe kudi don maganin abin.
Amma wani lokaci ana kashe kudin a kan tsaro ba ta tsarin da zai ba da da mai ido ba.

Misali miliyoyin da ake zargin an kashe na tsaro ta ofishin Sakataren gwamnatin Katsina, wanda abin a yi bincike ne mai zaman kanshi.
Ana zargin wasu kudaden da an yi amfani da su a tsarin da ya dace da Jihar Katsina ta zama mafi ingancin tsaro a fadin kasar nan.
Kodayeke ofishin na sakataren gwamnatin ya sha karyatawa da bayar da nasa bahasin.bayanin da har yanzu wasu basu gamsu dashi ba.
Maganar kare kai abu ne mai amfani, amma sai da tsari na masana.
Danjuma :shine mawallafin shafukan jaridun bisa yanar gizo na
Katsina city news@ www.katsinacitynews.com. jaridar taskar labarai@ www.jaridartaskarlabarai.com. the links news @ www.thelinksnews.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here