KARE KAI DAGA MAHARA: ME YA KAMATA A YI?

0

KARE KAI DAGA MAHARA:

ME YA KAMATA A YI?

….Sharhin Katsina City News

Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi ta maza, kuma ya yi abin da ya dace da ya fada wa jama’a a gaskiyar cewa kowa ya tashi ya kare kansa.

Maganar gaskiya ita ce, dogara ga jami’an tsaro jiran gawon shanu ne.

Idan kasa na fuskantar yakin sunkuru daga ‘yan sari-ka-noke, kowa ya zama soja, tsohon matsayi ne a tarihi.

A yakin basasar Nijeriya da aka yi a tsakanin 1967-1970, sai da aka karfafa mutane su kare kansu.

Lokacin da kasar Isra’ila ta mamaye kasar Falasdinu, Larabawa ‘yan kasar sun dau matakin kare kai ne, yayin da Yahudawa ‘yan mamaya, su ma Isra’ila ta ba su damar daukar bindiga don su kare kansu.

Hatta a kasar Birtaniya da aka mamaye yankin yammacin Ailand, sai da ta karfafa wa mutanenta da ke yankin su kare kansu.

A kasar Amurka da ayyukan ‘yan daba da na Mafia suka yi yawa, umurni aka bayar kowa yana iya kare kansa.

Don haka ba sabon sako bane, idan yanki yana cikin hali ko yanayi, amma me ya kamata a yi?

Abin da tarihi ya nuna shi ne, yankin da ke cikin halin ake zuwa a wayar masu da kai a ilmantar da su, a tsanake, a ilmance, a kuma koya masu yadda za su kare kan nasu.

Tsaffin masana tsaro za a samu masu kishi a yi jadawalin duk yankin da ke cikin matsala a tara matasansu da masu sha’awa a ilmantar da su, kuma a horas da su.

Malamai su yi masu jawabin rayuwa cikin kaskanci da mutuwa da daraja, a saka masu kishi da tsoron Allah. Sannan kowa ya koma garinsu ya zauna.

Da wannan kowa zai kare yankinsu da kishi, amma jami’an tsaron da ake kawo mana yawancinsu baki ne. Wasu ma ‘yan ko-ta-ware, ko-ta-waraye ne. Ba ruwansu da wani kishi. Wani lokacin suna ma fadan ne don tsira da ransu.

Maganar Gwamna kar a dauke ta da wasa, gaskiya ce, kuma ita ce mafita. Tarihi ya tabbatar da haka ake a baya, amma a yi shi bisa tsari.

Horon da za a bai wa yankunan da ke fama da matsalar ba wani kudin gaske zai ci ba in har za a yi abin da ikhlasi.

Wani kaso ne dan kadan daga kudin da ake kashewa na tsaro a ofishin Sakataren Gwamnatin Katsina.

Wannan ra’ayinmu ne a jaridun Katsina City News da Taskar Labarai.
Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
www.thelinksnews.com
07043777779 0813777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here