WASU MAHARA SUN KAI FARMAKI BATSARI TA JIHAR KATSINA.

0

WASU MAHARA SUN KAI FARMAKI BATSARI TA JIHAR KATSINA.
Daga misbahu Ahmad batsari
@ katsina city news

Da misalin karfe tara na daren ranar talata 17-08-2021 wasu gungun ‘yan bindiga masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa suka yima unguwannin Tanki da unguwar Malamai dake cikin garin Batsari a jihar Katsina dirar mikiya.

Sunyi harbe-harbe tamkar a fagen fama wanda ya ruda mafi yawan al’umar ciki da wajen garin Batsari, sun kama mutane masu yawan gaske, mata da yara kanana da magidanta.

Sai dai cikin taimakon Allah, da yawan mazan da suka dauka sun kubuto. Amma yanzu akwai mutane goma hannun su, matan aure bakwai, yaran goye biyu da magidanci guda daya. Sai dai mutane ukku sun gamu da ajaliyyar su sakamakon harin.

Dattijiya daya wacce aka labarta mana tana da hawan jini, kuma sakamakon harbe-harben jikinta ya motsa wanda nan take rai yayi halin shi, sai mutane biyu maza magidanta mazauna unguwar kwana ukku wadanda ake zargin sun yi taho mu gama ne da harbe harben da aka rikayi.

See also  YAN SANDA SUNYI BORE A BATSARI TA JAHAR KATSINA

Majiyar mu ta bayyana mana cewa lokacin da jami’an tsaro suka tunkaro su a guje sai wani ya harba bindigar toka, dalili kenan da yasa jami’an tsaro suka yi harbin da yayi sanadiyyar rasa rayukan mutanen biyu.

A wani labarin kuma, dandazon ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Dankar dake cikin yankin na Batsari, duka a ranar ta talata, inda suka sace dabbobin da suka hada da shanu, tumaki da awaki da yawansu bai gaza ma dari ukku ba, sunyi harbe-harbe kuma sun balle shaguna sun wasashe kayyakin masaruhi sun dora kan babura sun tafi salin alin
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here