MUTANEN BATSARI SUN KUBUTA DAGA WAJEN YAN BINDIGA
daga misbahu A batsari
@ katsina city news
Ranar talata ne ‘yan bindiga suka kai hari Batsari ta jihar Katsina, inda suka yi harbe-harbe tare da yin garkuwa da mutane da dama, galibin su matan aure.
Amma cikin ikon Allah da taimakon sa, sai labari yazo cewa, an sako su suna cikin garin Nahuta. Tun da sanyin safiyar juma’a 20-08-2021 aka je aka taho da su gida Batsari. Mun samu zantawa da daya daga cikin su, Kuma ta bayyana mana irin halin da suka shiga tun daga daukar su zuwa sako su. “Lokacin da suka tafi da mu, sun ratsa gonakai cikin sarkakiyar amfanin gona, ga duhun damina ga kaya da sauran su, amma a haka suka kora mu daji ba ko takalmi a kafar mu. Da suka kai mu inda suka kai mu sai wani daga cikin su yace mani wai yana so na, nace masa don Allah kayi hakuri ni matar aure ce, yace karya kike munafuka nan zanyi maki daki, rubuta mani lambar wayarki nace masa bani da waya yace karya ne, ai da ganin ki ke ‘yar boko ce. Bayan ya tafi sai wani yazo yace Kacalla yace ku bada lambar waya a kira dangin ku su kawo kudi a sake ku in kuma ba’a kawo ba kashe ku zamu yi.
ya dauko bindiga ya sake firgita mu, muka fadi muna kuka muna ahi muna cewa don Allah kuyi hakuri. Suka sake daka mana tsawa, sannan muka yi tsit.
Daga bisani Kuma wani ya sake ware mu ni da wata mata yace ku da ganin ku mazan ku masu kudi ne ko?
Muka ce masa Wallahi ba masu kudi bane yace karya kuke, ga jikin ku nan bul-bul. Bayan mun kwana ukku a hannun su sai wani yazo yace mana Kacalla yace zaa sake mu, amma ga sako mu gaya ma Sarkin Rumah, ya kashe banga in ba haka ba sai sun maida Batsari mazaunin birai (Kufai) don ba zasu daina kawo hari ba.
Waninsu Kuma yace mani, shi bai taba zuwa Batsari ba sai wannan karon kuma an tura su ne domin su kamo ‘yan banga, da basu same su ba sai suka kamo mu amma zasu sake dawowa sai sun kama su duka.
Kuma suka ce mana suna iya yin gayyar babura sama ga dari biyar su kawo hari Batsarin.
A ranar jumaa da yamma sai wanin su ya izo keyar mu gaba yace zai kawo mu hanyar da zata kaimu Nahuta. Da yake shi yana kan babur ne, mu kuma muna tafiya a kafa har na taka kaya kuma gashi na gaji, sai yace inzo ya dauke ni da wata daga cikin mu ya isa damu, hakan akayi kuwa bayan ya kaimu wani waje yace mu jira yaje ya taho da sauran (matan guda ukku), da muka ga ya dan jima bai dawo ba, kuma gashi magariba tayi, muna gudun kada wasu su sake Kama mu, sai muka kama wata hanya muka bi, can sai muka ga mun isa kusa da wani gida, muna yin sallama muka ce nan ne Nahuta? sai muka ga ashe wani gidan fulani ne, nan take muka yi turus muna kyarma tsoro ya sake kama mu, sai suka ce mana ku shigo kada kuji tsoro daga daji kuke?
Da muka shiga suka bamu fura muka sha, sannan suka ce to ku kwanta nan ba’a hira, muka kwanta, da gari ya waye suka bamu ruwa muka yi wanka sannan suka bamu kaya muka canza Kuma suka bamu abinci muka ci, maigidan ya kawo naira dari biyar ya bamu yace idan mun isa Nahuta mun hau dan acaba ya kaimu gida.
Muka yi godiya, matar sa tayi mana rakiya ta dora mu hanyar Nahuta. Muka isa Nahuta daga nan aka kaimu gida. Su kuma ‘yan’uwan mu ashe tuni sun riga mu zuwa gida, domin har an fara koke-koke ana zaton ko sun ruke mu ne.”
Ta bayyana cewa adadin wadanda suka kawo harin sunkai arba’in, kuma akasarin su yara ne masu kananan shekaru (16-17).
Tace sun basu shinkafa da amma suka kasa ci, sai suka debo geza zasu basu kashi wanda hakan ya bb tilasta suka ci abincin, kuma sun basu kunu kafin su samu ‘yanci. Sannan a bisa gayen geza suke kwana maimakon tabarma ko katifa ga sanyi ga lemar damina, ga kwari masu cizo ga babu mayafi, haka suka kasance har Allah ya ‘yantar da su. Sun sha wahala sosai ga fargaba ga tsoratarwar da suke yo masu ki da yaushe suna cewa zasu kashe su, har ma sun nuna masu wani rami da suka ce nan suke jefa duk wanda suka kashe, kuma sunga alamun hakan.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245