BA BAJINTA BACE YIN KUKA A ZAUREN MAJALLISA

0

BA BAJINTA BACE YIN KUKA A ZAUREN MAJALLISA.
Daga Abdurrahman Aliyu

Zauren majallisar dokoki ya Allah na jiha ko na tarayya ba a samar da shi domin zaman makoki ko jaje ba, bai wanzu don kawai wani dan majallisa ya zo ya rika rusa kuka ba, an samar da shi ne domin samar da mafita da juma jajircewa domin tabbatar da an yi abinda ya dace.

Kuka bai daga cikin tsarin duk wani jajirataccen mutum, lusaranci ne mutane su zabeka domin kare muradan su ka buge da yin Allah ya isa a zauren majallisa, lallai wannan gazawa ce. Kuma kamata yayi duk mai wannan halin ya sauka daga kujerarsa domin ba Allah ya isa aka zabe shi yayi ba, an zabe shi ne ya kare muradan al’umma ba wai ya rika cin albashi a wata yana Allah ya isa ba ko fashewa da kuka, in wannan ne kowa ma zai iya daga gida.

Asali ma kuka ga mutumin da ya haura shekara 40 alamomi ne na yaudara.

Kowa ya san akwai matsalar tsaro a kasa baki daya ba ma jihar Katsina ba. Amma a matsayinku na wadanda mutane suka zabo suka ce ku kare masu muradansu, kuna da hanyoyi da yawa da zaku iya magance matsalar bakin iyawarku ba wai Allah ya isa ko kuka ba.

Yana da kyau ku sani tun da gwamnatin tarayya kuke kalubalanta akwai hanyoyin da zaku nuna mata rashin gamsuwa da kokarinta na farko ita ke nada shugaban ‘Yansanda tunda an gaza samun abin da ake so a karkashin wannan zaku iya rubutawa a sauya maku shi a kawo wani domin ku jaraba shi, kuna da wannan damar.

Zaku iya rubutawa ku tsaya tsayin daka sai an cire maku shugaban sojijin da ke jagorantar jihar da shugaban jami’an tsaro na farin kaya da duk wani mai ruwa da tsaki kan tsaro wanda baku gamsu da aikinsa ba, amma hakan ya gagara sai hayaniya da koke-koke da ba zai haifar da da mai Ido ba.

Daga karshe in har kuna ganin ba zaku iya neman a sauya maku jami’an tsaron ba to hakkinku ne a shiga daji da ku domin ganin yadda jami’an tsaron ke gudanar da ayyukansu, ta yadda in kun koma mazabunku zaku yi masu bayanin cewa ana baki kokari.

Amma in kun zabi Allah ya isa to ai muma ku muka tura kuma bamu ga wani amfaninku ba, muma sai muce Allah ya Isa tsakaninmu daku da irin wannan hali da muke ciki.
Abdurrahman Aliyu marubuci ne daga karamar hukumar Rimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here