Kano, Musulunci, Iran da Faransa

0

Kano, Musulunci, Iran da Faransa

Daga Fatuhu Mustapha

(In mutane ba su yi hankali ba, sai wata rana an kawo musu abinda ba siyasa bace an ce musu siyasa ce)
—- Malam Aminu Kano

Babban abin takaici shi ne, yadda duk da kuzun ilmin addini da mutanen Kano ke yi, amma ba hanya mafi sauki da za ka raina wa mutanen Kano hankali irin ka biyo su ta hanyar addini. Malam Lawan Kalarawo ya tafa fadar wata magana makamanciyar wannan, yayin da yake cewa “Kai mutumin Kano, in ana so a raina ma hankali, sai a hada ka da Allah, kai kuma sai ka yadda a yi maka wayo”. Ban yi mamaki ba da Karl Marx ya ce “addini ba wani abu bane, illa hanyar shagaltar da talakawa”. Anan ba ina so Ince adddini karya bane, amma a yau ya zama wani sinadari da malamai da yan siyasa ke amfani da shi, domin su kare danne talaka kar ya fuskanci kalubalen da ke gaban sa a rayuwa. Abubuwan da suka faru kwanakin nan, ya kara tabbatar da haka. Kama daga rikicin Sheikh AbdulJabbar da wasu gungu na malaman Kano, ya zuwa wata yarjejeniya da gwamnatin Kano ta kulla da Kasar Faransa.

In bamu manta ba, a shekarun baya zamanin gwamnatin Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Gwamnatin Kasar Iran ta kulla wata yarjejeniya da kasar Jihar Kano, inda suka amince za su bayar da guraben karatu kyauta a jami’o’in kasar, ga dalibai masu shaawar karatun kimiyya da fasaha. Daga jin wannan yarjejeniya, sai wasu malamai a Kano suka yi caa akan gwamnati, suka nunawa cewa hakan anyi shi ne domin a maida matasan Kano yan Shia. Hakan ya sanya Kwankwaso ya ki karbar tayin guraben da kasar ta Iran ta yi masa. Yan kwanaki kadan bayan nan sai muka samu sanarwar, gwamnatin Kano za ta biyawa mata har dari su je Saudiya su koyo aikin jiyya a jami’o’in kasar. Abin mamakin babu malami daya daga bangaren Shia ko dariqa da ya soki abin, da sunan cewa za a maida matasan Kano Wahabiyawa. Baya ga kowa ya san da cewa, kalilan ne suke dawowa daga karatu daga Saudi ba tare da an sanya musu aqidar wannan dariqa ta wahabiyanci ba. (Bani da matsala da mutum ya zama Bawahabiye, kowa yana da zabin ya yi abinda yaga shi ne daidai a rayuwar sa).

Babban abin takaicin shi ne, yadda wannan surutai na malamai ya sanya Kano ta yi asarar wannan dama da kasar Iran ta bata. Na farko dai, akwai yan Shia bila adadin yan Kano da za su iya amfana da wannan garabasa, na biyu malaman nan na iya kashedin basu yadda a tura yaran da ba yan Shia ba. Na uku, ko anje Iran ko ba a je ba, yan Shia na nan a Kano jingim. To a yanzu wa ya yi asara, Iran ko Kano. Ina ruwan mutane da aqidar da likita ya ke bi, ko wace aqida injiniyan da ya gina titin Kano zuwa Abuja ya ke kai? Hasali ma kamfanonin da ke ayyukan tituna a Nigeria galibi ba na musulmi bane. Wannan kenan!!

See also  YADDA AKA DAKILE SATAR UMARU DIKKO

Ana cikin kukan targade sai ga karaya ta samu. Domin a lokacin da gwamnatin Khadimul Islam ke dukan kirji tana nunawa duniya ita ce gwamnatin da tafi kowa son Manzon Allah (SAW), tun bayan da ta kama ta kuma gurfanar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gaban kotu tana tuhumar sa da ya ci mutuncin manzon Allah (SAW), sai kuma ga mai dokar bacci ya buge da gyangyadi, ina zaton dai a yayin da ake yabon gwamnatin da iya sallah, sai ga shi ta gaza alwala. Domin kuwa katsam sai muka samu labarin gwamnatin ta Khadimul Islam ta kulla wata yarjejeniya da gwamnatin Faransa, karkashin jagorancin Shugaban da ya kira sunan Manzon Allah ya ci mutuncin sa. Har ta kai ga wasu malamai na kiran da a kauracewa duk wani abu na kasar Faransa. Sai da ma mutane suka ringa kiran da lallai a sauya sunan titin France Rd zuwa wani suna, saboda tsananin kyamar da mutane suka nunawa faransa. Amma kuma sai ga gwamnatin da tafi kowa son manzon Allah (saw) ba wai kawai ta kulla yarjejeniya da kasar ta faran sa ba, har ma ta fara karbar somin tabi na Miliyan 10.

Ko a yan kwanakin nan, mai baiwa gwamnan Kano shawara akan addini, Malam Ali Baba A Gama Lafiya, ya shiga Radio yana amfani da waccan rikici na Sheikh Abduljabbar, yana nuna yadda ubangidan sa Khadimul Islam ya nuna tsananin soyayyar sa ga manzon Allah, amma kuma ga babban abokin adawar sa Rabiu Kwankwaso da mabiyan sa sun ki cewa uffan akan batun. Inda ya nuna cewa hakan na nuna Ganduje ya fi Kwankwaso son Manzon Allah (SAW).

In an koma ta daya gefen, hausawa kan ce, akuya ko bata haihuwa ta fi kare. Domin dai, wurin nuna kishin addini kasar Iran ba baya ba ce, domin ita ce kasa daya tilo da ta bayar da fatawar hukuncin kisa akan Shaidanin marubucin nan da ya ci mutincin Annabi Muhammadu (SAW) a littafin sa maisuna Satanic Verses. Ko banza dai in har gwamnatin da gaske son annabi take, to kuwa ya kamata ta janye wannan yarjejeniya ta kuma maidawa kasar Faransa awalajar ta da tuni ta karbe. In kuma ba haka ba, to ko shakka babu abin duk tatsuniya ce kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here