WAKE AIKI A KANKARA SANATA YAKUBU LADO KO GWAMNATIN TARAYYA?

0

WAKE AIKI A KANKARA
SANATA YAKUBU LADO KO GWAMNATIN TARAYYA?
muazu hassan
@ katsina city news
A satin da muke ciki hotuna da bidiyo suka cika shafukan sada zumunta na yanar gizo akan wani aikin hanyoyin cikin garin Kankara da akeyi.
Wasu jaridun yanar gizo ciki har da katsina city news sun dauki hotunan suka buga a matsayin wani aikin Alheri da wani Dan siyasa keyi ma al ummarsa kyauta.
Labarin ya jawo hankali da motsa jijiyar wuya, bayan da jaridar katsina city news ta buga hotunan.


Dan majalisar tarayya mai wakiltar mashi da Dutsi Alhaji Mansir Ali mashi ya bayyana ma daya daga cikin editocin jaridar cewa wannan aikin da Yakubu lado keyi na gwamnatin tarayya ne
Kuma an saka shi a cikin kasafin kudin 2021.Dan majalisar ya nuna ma editan takardun kasafin kudin na 2021.
Inda a ciki aka Sanya aikin hanya a Kankara jahar katsina kan kudin naira milyan dari biyu da tamanin.
Wannan aikin shine Wanda sanata Yakubu lado ya samo a matsayin dan kwangila daga gwamnan tarayya amma yake son ya karkatar dasu inji Alhaji Mansir ali mashi a matsayin aikin shi.
Dan majalisar ya kuma bankado wani aikin gwamnatin tarayya na naira milyan dari biyu da za a Gina dakunan kwana a wata makaranta mai zaman kanta ta horon aikin jinya.mai suna health technology Kankara.
A takardun da editan katsina city news ya gani an saka naira milyan dari biyu a wannan makarantar da ba ta gwamnatin jaha,tarayya ko karamar hukuma ba.
Binciken katsina city news ya gano makarantar ta wasu mutane ce kuma ko cikakken lasisi basu Samu ba.
Amma sun fara karatu da wani gidan da suke haya mallakin sanata Yakubu lado. Sannan sun saka sanata Yakubu lado a matsayin daraktocin makarantar.
Kwatsam sai ga sunanta kasafin kudin gwamnatin tarayya za a yi mata aiki na naira milyan dari biyu.
Shima wannan aikin Dan majalisar tarayya Alhaji mansur Ali mashi ya rubuta koken a dakatar dashi .a maimakon a gidan ma wata makaranta mai zaman kanta aikin naira milyan dari biyu gara ayi wani aikin cigaba da kudin a karamar hukumar Kankara.
Wasu na zargin hatta ayyukan da akayi a garin Dan marke duk ta irin wannan hanyar akayi aikin.
Katsina city news ta gano an saka aiki kusan na bilyan daya a karamar hukumar Kankara a kasafin kudin 2021.
Daga cikin su akwai wata cibiyar koyon sana oi ta matasa.da wasu fitulu masu amfani da hasken Rana a wasu garuruwan Kankara.
Amma duk ayyukan nan yan majalisar tarayya na Kankara da sanatan yankin Kankara bai san da su ba.wanda ake zargin kamar wata karkatar da kudi ake son yi da wayon aiki.
Katsina city news mun tuntubi sanata Yakubu lado Dan marke don jin ta bakin shi bamu samu amsa ba.mun aika masa sako ta whaazp shima muna jiran amsa.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here