ZARGIN BA ‘YAN BINDIGA RAHOTO

0

ZARGIN BA ‘YAN BINDIGA RAHOTO;
…Wadanda aka kama bincike ake yi

-Sharhin Katsina City News

Kwanan nan jami’an tsaro sun samu nasarori da yawa a kan ‘yan bindigar da ke addabar mutane.

Sannan a kuma kwanan nan jami’an tsaro sun kama mutane da yawa wadanda ake zargin suna ba ‘yan bindiga bayanai, wadanda ake bincike yanzu haka a kan su.

Watanni baya jami’an tsaron farin kaya na DSS sun yi irin wannan nasarar ta kama wadanda ake zargi da kokarin kafa kansu a cikin al’umma da samun gindin zama da kuma zama wakilai masu kai rahoto ga ‘yan bindigar daji.

Wannan aikin na jami’an tsaron farin kaya na DSS da suka yi nasarar samu a cikin birnin Katsina na daga wani aiki da ya kawo wa cikin birnin zaman lafiya.

Kamar yadda wani masanin harkar tsaro ya fada wa jaridunmu, ‘yan rahoton ‘yan bindiga ne suka samu wuraren zama a tsakiyar mutane suna sana’o’i daban-daban, kuma suna lura da kai-komon mutane. Kungiyarsu ce aka fasa aka yi nasarar kama su da taimakon Allah.

Kwanan nan jami’an tsaro sun sake kama wasu da ake zargi masu yawan gaske, kuma ana bincike da nufin tantance su.

A wannan karon abin da ya fi jan hankali shi ne kama ‘yan kwamitin sasanci da gwamnati ta san da aikinsu na Karamar Hukumar Batsari.

A iya binciken da jaridar nan ta yi, wadannan ‘yan kwamitin, Karamar Hukumar Batsari ce ta kafa su bisa amincewar gwamnatin Jiha, kuma a baya sun taka muhimiyyar rawa wajen shiga gaba a yi magana da duk wani dan bindiga da ke daji.

Sun kuma taka rawa wajen kokarin sallamo wasu da ‘yan bindigar suka dauke.

Wata kofa ce wadda aka bude ta magana tsakanin ‘yan bindiga da gwamnati ta hanyar su. Kuma an sha sanya su ayyuka suna yi da yardar jami’an tsaro da izinin Karamar Hukuma da masu kasa a Batsari.

Aikin su ya tseratar da rayuka da yawa. Irin wannan kafa da akan samar, kuma a bari ta magana ba sabon abu ba ne a yaki a duk duniya.

A Maiduguri shekaru masu yawa gwamnati da jami’an tsaro sun san wadanda kan yi magana da manyan Boko Haram, kuma suka kyale su a matsayin kafa ta isar da sako tsakanin su.

Ko a siyasar duniya lokacin da Amurka ke yaki da Taliban a Afghanistan, tana kuma magana da su ta jami’an kasar Qatar a birnin Doha.

Don haka a tsaro, kafar magana ba laifi ba ne in har an tabbatar wanda ke shiga tsakani ba munafuki ba ne.

A tarihin tsaro, Alhaji Ibrahim Katsina, mai ba Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari shawara a kan harkar tsaro, akwai inda ya ciri tuta.

Shi ne wanda a lokacin da yake Darakta na DSS a Jihar Kebbi, har ya bar kujerar, Boko Haram ba ta taba ta da bom a Jihar ba. Ba ta kuma taba kai hari ba.

Sirrin da ya yi amfani da shi shi ne, bude kofar magana ya yi da wasu ‘yan Boko Haram din da aka kamo masa.

Matsayinsa na mai ba Gwamna shawara a fannin tsaro da wasu hanyoyin da ya bullo da su, sun taimaka wajen rage halin da muke ciki fiye da kima. Daga cikin hanyoyin da ya yi amfani da su akwai bude kofar magana da wasu ‘yan bindigar.

Gaskiya magana abin da mutane da yawa ba su sani ba, hanyoyi daban-daban na magana da kungiyoyin Fulani da iyayensu da Ibrahim Katsina ya bude, sun taimaka wajen rage barnar da ke faruwa ta ‘yan bindiga a Katsina.

Yana aiki tsakaninsa da Allah, kuma bisa ilmin tsaro, tare da tafiya da jami’an tsaro abokan aikinsa. Bai saka siyasa a aikin nasa ba, kamar yadda ake zargin wani ya rika yi a baya.

Mun kawo wannan ne a matsayin misali don tabbatar da cewa shiga tsakani, in ba ana da tabbacin mai kai-komon munafuki ba ne, ba laifi ba ne.

Kuma ayyukan da ‘yan kwamitin sasanci na Batsari, wadanda suke tsare a yanzu, shi ma ba laifi ba ne.

Amma tun da an kama su, ana kuma bincike, da yardar Allah gaskiya za ta yi halin ta.

Abin tsoro a nan kar abin da aka yi masu ya zama mummunan darasin da gobe duk wanda aka sanya wannan aikin zai ki yi, ko kuma in ya amshi aikin, ya ki yin abin da ya dace.

Ya kamata iyalai da ‘yan’uwan wadanda aka kama na ‘yan kwamitin sasancin Batsari su sani, su kuma sa yi hakuri, bincike ake yi. Ba cewa aka yi an kama su da laifi ba. Jarabawa ce daga Allah, su mika al’amarinsu ga Allah.

Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com
07043777779 08137777246
Email; katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here