AN SOMA BA DA HAYAR RAGON SUNA A KANO.

0

KO DA ME KA ZO, AN FIKA.

AN SOMA BA DA HAYAR RAGON SUNA A KANO.

Gidan Rediyon Dala FM da ke Kano, a wani shiri mai suna BABA SUDA na daren Jiya, ya ruwaito cewa, yanzu haka an fito da tsarin bada hayar RAGON SUNA ga masu bukata.

Rahoton, ya ce wadanda aka yiwa haihuwa, alhali ba su da ragon suna, kan tuntubi mahautan da su ke da alaka.

Daga nan akan yi yarjejeniyar Sayen hanjin dabban da za a yanka domin sayarwa. Shi ne kadai na wanda aka yiwa haihuwar.

Rahoton ya cigaba da cewa daga nan mahaucin kan bada Murgujejen ragon da yake shirin yankawa na tsire ko wanda za a sayarwa jama’a danye. Za a kai ragon Gidan da aka yi haihuwar a ranar suna da safe.

See also  Senata Orji Uzor Kalu Ya Saka Gasar A Shafinsa Na Kafar Sada Zumunta.

Za a fito da Ragon, a yanka a fede a gyara akan idanuwan mutane, a matsayin ragon suna. Sannan kuma, za a kwashe Kayan Ciki a kai cikin gida a cigaba da suya. Gangar jikin ragon kuwa, akan rataye shi kamar yana jiran suya.

Sai dai Kuma, da zaran an yi yinin suna Mutane sun ga rago a rataye, da an watse, akan faki Idanuwa, a dauki gangar Jikin ragon nan a mayarwa mahauci da Kayan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here