DAN MAJALISAR TARAYYA DAGA KATSINA…YA GINA OTEL A MARADI KASAR NIJAR.

0
7

DAN MAJALISAR TARAYYA DAGA KATSINA…YA GINA OTEL A MARADI KASAR NIJAR.
@ katsina city news
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin batsari, safana da Dan Musa.Alhaji Ahmad dayyabu safana ya Gina katafariyar otel a garin maradi, jahar maradi, ta kasar jumhuriyar Nijar.
Otel din mai dakuna da yawan gaske tana daga cikin otel mafi tsada a kasar Nijar.
A karshen satin da ya gabata akayi gagarumin bukin bude otel din.inda bikin ya samu halartar sakataren gwamnatin jahar katsina. Alhaji Mustafa inuwa, da wasu masu ba gwamnan katsina shawara .da kakakin jam iyyar APC ta jahar katsina.abu Gambo Dan Musa.
A iya binciken jaridun katsina city news, ba su gano wuri daya da Dan majalisar ya samar a Najeriya ba.wanda ya ke ba matasa aiki. A iya binciken mu a mazabar shi inda yake wakilta, basu gano makaranta ko asibiti da ya Gina da kudinshi ba,domin talakawan yankin.
Dan majalisar yanzu yan cikin shekarunsa na takwas a bisa kujerar.
Dan majalisar shine ke wakiltar yankin da yafi fama da matsalar harin yan ta addar fulanin daji.ba a jin yayi gangamin kai jaje.ko ta aziyya ba.
Munyi kokarin magana dashi akan zabin sa na na Gina otel a nijar da bukin bude a dai dai lokacin da mutanen sa na cikin ukubar yan ta addar fulanin daji amma mun kasa samun shi.mun aika masa da sakon kar ta kwana ta waya ,ba amsa.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here