Alfanun albasa ga lafiyar jiki

0

SAU da yawa, mu kan danganta albasa ne da cewa ta na kawo zubar hawaye idan mun yanka ta, ko kuma ana amfani da ita ne wajen girka abinci kaɗai. Hakan gaskiya ne, to amma ko kun san cewa za ku iya amfani da albasa wajen wasu abubuwan daban? Alal hakika, albasa na da tarin amfani wajen yaƙar cututtuka da dama na yau da kullum.

Wata shahararriyar likitar lafiyar iyali da ke birnin Los Anjalis a Amurka mai suna Dakta Lauren Feder, ta tabbatar da cewa albasa ta na da amfani a jikin ɗan’adam. Albasa ta kan warkar da mura, ciwon mafitsara, ciwon kunne, ciwon haƙori, ciwon ciki, ciwon zuciya, ɗaurewar ƙirji, rashin sha’awar cin abinci, ɗaurewar hanyoyin jini, hawan jini, ciwon daji, cutar fatar jiki, da sauran su.

Likitoci sun ce albasa na ɗauke da wani sinadari da ke kashe dafi.

Wani nazari da aka yi a cikin 2019, wanda aka wallafa a mujallar ‘Asia Pacific Journal of Clinical Oncology’, ya kwatanta mutum 833 da ke fama da ciwon daji na dubura da kuma mutum 833 waɗanda ba su da wannan cutar. Sai masu binciken su ka gano cewa yiwuwar kamuwa da cutar dajin ta fi rashin ƙarfi da kashi 79 cikin ɗari a wajen su ke cin ganyayyakin da su ka danganci albasa.

A ƙasar Chaina, an daɗe ana amfani da albasa wajen yaƙar cututtuka. A cewar Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), Chaina ta fi kowace ƙasa noman albasa. Hakan bai rasa nasaba da yadda ‘yan Chaina su ka ɗauke ta a matsayin wata muhimmiyar hanyar samun lafiya daga cututtuka.

Albasa kala-kala ce

ALBASA A SAFA

Yawanci an ɗauka cewa cin albasa a cikin abinci ne kaɗai hanyar da ake samun alfanun albasa. To akwai wata hanyar. Wannan kuwa ita ce yin amfani da ɗanyar albasar a jikin fatar ƙafa.

Yadda za ka yi shi ne, na farko dai ka ɓare albasa, sannan ka yanka ta gida biyu, sai ka maƙala kowane ɓari a jikin tafukan ƙafar ka, daga nan sai ka sanya safa, kafin ka shiga barci. Idan ka tashi daga barcin kuma, to ka goge ƙafar, ka wanke ta, don fitar da warin albasar.

See also  Hukumar 'yansanda ta dakatar da taron rufe yakin Neman zaben Bakura

Albasa kala-kala ce. Akwai ja, rawaya, fara, ruwan ɗorawa, da sauran su, to amma kowace iri aka samu ta na da matuƙar amfani ga jikin ɗan’adam. Sai dai masana sun bada shawarar cewa kada a yi amfani da albasar da ta sha takin zamani ko feshin kashe ƙwari wajen noma ta, domin kuwa irin waɗannan magungunan su kan shiga jikin mutum su jawo matsalar da ba a zato. A yi amfani da albasar da aka noma a lambu, ba irin ta gwaji ɗin nan ba.

Ga wasu daga cikin cututtukan da albasa kan warkar.

ƘWAYAR BAKTERIYA

Kimiyyar magunguna ta tabbatar da cewa akwai sama da zaren halitta guda 7,000 a cikin tafin ƙafar mutum waɗanda su ke da alaƙa da dukkan jiki. Hakan ya sa idan ka saka albasa a cikin safar ƙafar ka, amfanin ta ga dukkan jikin ne, ba ga ƙafar ita kaɗai ba. Da zarar ka saka albasar a cikin safar ka, za ta fara aikin tsakake maka jiki daga ƙwayoyin cuta. Za ta tsotse ƙwayoyin bakteriya da na sauran cututtuka daga jikin ka, kuma saboda fatar jikin ƙafar ka ba ta da kauri, bakteriya mai amfani da sauran sinadaran da ke ƙara lafiya za su shiga cikin jinin ka da sauri. Ta haka ne albasar za ta inganta maka jinin jikin ka. Kuma duk hakan na faruwa ne a lokacin da ka ke shan barci har dam minshari!

Dakta Lauren Feder

SANYI

Idan ka saka albasa cikin safar ƙafar ka kafin ka yi barci, za ka samu waraka daga ciwon sanyi irin su mura a cikin hanzari. Albasa za ta taimaka wa jikin ka saboda sinadaran ƙarin lafiya da ke cikin ta. An san cewa albasa na tsotse duk wani wari kuma ta inganta iskar da mu ke shaƙa. Idan ka saka albasa a cikin safar ka kafin ka kwanta barci, za ta tsotse ƙwayoyin cuta tare da inganta jinin jikin ka.

A jaraba a gani. Hausawa sun ce da rashin tayi a kan bar arha. Yi ƙoƙari ka saka albasa a cikin safar ka idan za ka kwanta a yau!

Copyright @ Fim Magazine. All rights reserved

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here