RIKICIN PDP A KATSINA; BA A RUFE KOFAR SULHU BA

0

RIKICIN PDP A KATSINA;
BA A RUFE KOFAR SULHU BA
……….In ji Shugabanninta
…Martanin ga katsina city news

Muazu Hassan
@Katsina City News

Shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Katsina, sun musanta labarin da jaridar Katsina City News ta fitar ranar Litinin 6/9/2021 mai taken: ‘Rikicin PDP a Katsina, an rufe kofar sulhu’.

A wata tattaunawar wayar ta tarho da babban Edita Jaridun ya yi da Shugabannin jam’iyyar PDP na Katsina, sun ce labarin da jaridar ta bayar ba haka yake ba, kuma a sunkuye ta same shi, ba kamar yadda abin ya faru ba.

Shugabannin PDP din suka ce lallai ne an yi zaman Kwamitin Zartarwa na jam’iyya, wanda Wakilan da suka halarci taron sun kai mutum 80 ranar Lahadin da ta gabata a babban ofishin jam’iyyar da ke titin zuwa Kano.

Suka ce a zaman an yi awa daya babu mintuna kadan, kamar minti 55.

A lokacin zaman, kamar yadda suka ambata, wanda ya fara magana shi ne Shugaban jam’iyyar, Alhaji Salisu Yusufu Majigiri, wanda ya yi mintuna 23.

Daga nan sai Sanata Yakubu Lado Dan Marke ya yi magana ta mintuna uku kacal.

Daga nan sai aka bude zauren kowa ya fadi albarkacin bakinsa.

Shugabannin sun ce tabbas an kawo maganar sulhu da ake yi da ‘yan PDP a-gyara, wanda aka bukaci mahalarta taron su fadi ra’ayinsu a kan yarjejeniyar da aka yi da su.

Shugabannin suka ce a ka’ida dama wannan zaman shi ne zai yanke hukuncin karshe na yarjejeniyar da aka rubuta.

Suka ce kowa ya ba da tasa shawarar. Daga karshe aka ce a daga hannu ga matsaya biyu da ake da ita.

Kamar yadda suka shaida mana: “Matsayar farko in aka ce za a ba ‘yan a-gyara wasu mukaman da wasu ke sama za a haifar da wata sabuwar matsala, har da ta shari’a, amma a canza matsaya a kan duk lokacin da damar wani mukami ta samu a ba su. Misali canza sheka ko mutuwa”, in ji shugabannin.

Suka ce a matsaya ta biyu kuma, za a bi yarjejeniyar da aka tsara ta ba su wasu mukamai a Jiha da Kananan Hukumomi. “A kan wadannan matsaya guda biyu aka ce a daga hannu a kidaya masu goyon bayan kowace matsaya”, in ji majiyar tamu.

“Aka fara kiran matsayar sulhun takardar da aka yi babu wanda ya daga hannu.

Sai aka koma kan ta a ba su duk wani mukamin da ya samu a cikin jam’iyya a Jiha ko Kananan Hukumomi, a nan ne kowa ya daga hannu ba wanda ya ki amincewa”, in ji shugabannin.

A kan haka aka ce Wakilai su samu Wakilin bangaren PDP a-gyara, Malam Lawal Rufa’i Safana su shaida masa matsayar da aka cimma, kuma hakan aka yi

Shugabannin suka ce kofar sulhu a bude take, kuma za a ci gaba da yin sa, tare da bai wa duk ‘yan jam’iyya hakkinsu.
Har zuwa rubuta rahoton nan shugabannin PDP a gyara basu fitar da matsayarsu ba.wani daga cikin su ya shaida ma wakilanmu cewa .sai sun Kira taron kowa sun kuma ba kowa hakkinshi a bangaren nasu.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here