ZA A MAIDA MAKABARTUN KATSINA NA ZAMANI

0

ZA A MAIDA MAKABARTUN KATSINA NA ZAMANI
…Taron kwamitin da awa na jaha
@ katsina city news
An bayyana cewa wata kungiya mai suna crystal Muslim organisation zata kawo dauki don mayar da makabartun jahar katsina na zamani.
Babban jojin jahar katsina da babban alkalin alkalai na jahar katsina suka fadi haka a yau wajen taron kaddamar da kwamitin masu da awa na jahar katsina da gwamnatin katsina ta kafa.
Anyi taron kaddamarwar a dakin taro na babbar kotun jaha dake titin zuwa garin Daura a yau litinin. 13/9/2021.
A jawaban da akayi an nuna halin da jaha da kasarmu ke a ciki da awa ce mafita gareta.
An kafa kwamitin da awa na jaha ne Wanda ya kumshi malamai daban daban,bisa bukatar haka da aka kaima gwamnan katsina, kuma ya amince da hakan.
A wajen aka bayyana cewa komai yana tafiya da zamani amma banda makabartun mu.don haka daga aikin da aka ba kwamitin harda kokarin wayar dakan jama a yadda zasu kula da makabartun mu.
Wata kungiya mai rassa a jihohi da dama ta bayyana yadda ta kai ma gwamnan katsina bukatar Amincewa na mayar da makabartun jaha katsina na zamani.
A fadar su, gwamnan ya yi na am, ya kuma basu damar su zo da tsarinsu.
Kungiyar mai suna crystal Muslim organisation wadda a matakin jaha mai shara a Musa danladi Abubakar yake shugabanta. Sun nuna mahalarta taron bidiyon yadda zasu mayar da duk makabartun da sukayi ma aiki.
Makabartun mu, zasu zama akwai ofishin gudanarwa,da dakin wankan gawa.dana ajiye gawa.da sito na ajiye kayan Gina kabari.da wurin ajiye motoci mai kyau.da wurin sallar gawa.za a fitar da hanya wadda ba sai an taka kabari.
Kungiyar ta Nemi a bata fili Wanda zata fara da Gina wannan makabarta ta zamani,da kuma gyaran wadanda ake dasu.
Kungiyar tace ya yanta zasu bada gudummuwar aikin da tafiyar da duk inda suka gyara.
Wannan kwamitin na da awa zai fara aiki gadan gadan, kamar yadda aka Dora masa nauyi.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com 07043777779 081377777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here