WA ZAI CECI JAMI’AR UMARU MUSA YAR’ADUA KATSINA?

0

REPORTERS DIARY

WA ZAI CECI JAMI’AR UMARU MUSA YAR’ADUA KATSINA?

Bayan da jaridun mu suka kammala bincike akan halin da jami’ar Umaru Musa ke a ciki kuma muka yi zaman editocin jaridun akan sakamakon binciken, bisa ka’ida ta aiki abin da ya rage shi ne jin bahasin shugaban jami’ar Farfesa Sanusi Mamman.

Nan ne na daukar ma kaina neman ji daga gareshi a madadin jaridun domin mu cika ka’ida ta aikin jarida da kuma kammaluwar binciken da mukayi da fitar da rahoton abin da muka gano.

Isa ta harabar jami ‘ar nag a motar VC a inda ake ajiye ta, na tabbatar yana a ciki kuma naji dadi, nayi tsammanin zan samu ganin shi, muji ta bakinshi mu yi wa rahotonmu adalci.

Ina isa ofis aka ce baya a ciki, na tambaya “yana makaranta?” Aka ce baya ma a garin. “Amma me ya sanya aka ajiye motar kamar yana nan?” A kace mani haka yake. “Yaushe zai dawo? Yaushe zan iya samun shi a ofis?” ba wanda zai iya baka amsa.
Haka na tafi a ranar ban yi nasara ba.

Zuwa na uku, amsa daya nake samu bayanan, kayi hakuri ka sake dawowa, koda naga satin ya kare. sati mai shigowa na canza salo ita ce in rubuta takarda bisa takarda mai kan sarki na jaridunmu.
Da sako a takaice kamar haka:
“Muna son ganinka domin amsa tambayoyin wani bincike da muka yi wanda muke son fitarwa muna fatan zaka bamu lokacin da yayi maka ko ka bamu dama ko da ta waya ne muyi magana da kai”.

Da kaina na kai wasikar aka kuma buga mani shaidar an karba. Na taho ina jiran amsa,babu har yau da wannnan bayanin nawa ya fito. Ya ga wasikar, an tabbatar mani ya ganta. Dalili ya zauna a ofis kuma duk wasikun da aka kai masa tare da wasikar ya fito dasu zuwa inda ya dace banda wasikar mu.

Lokacin da tsohon VC ya kare, kungiyoyin na jami’ar da masu ruwa da tsaki sun yi ta kira da kokarin a ba dan cikin gida ya zama shugaban jami’ar, an yi kiraye-kiraye da zaune-zaune akan hakan.

Don haka, da Farfesa Sanusi Mamman ya zama ma’aikata da malamai da dalibai sun masa gagarumar maraba da fata ta gari.

An sa rai aga wani cigaba da gagarumin canji kamar yadda ake tsammani.
Kasa da shekara daya jami’ar na gab da shiga wani yanayin kama hanyar durkushewa in ba a dauki matakin gaggawa ba.

A bincikenmu wanda sama da kwanaki goma muna bin shugaban muji ta bakin shi ba muyi nasara ba mun ci karo da bayanai da takardu masu daga hankali wanda ya dace gwamnan Katsina ya kawo wa jami’ar daukin gaggawa da karfin ikonshi kafin lamarin ya kara muni.

Mun samu takardun korafi daban-daban wanda aka rubuta wa hukumar gudanarwa ta jami’ar cikin hadda wadda gamayyar kungoyoyin fararen hula na jihar Katsina suka rubuta. Da wata da aka rubuta wa gwamnan Katsina ka tsaye.

Gwamnan Katsina ya bada shelar a dau duk wanda ya gama da First Class Degree a jami’ar.

Shelar da duk duniya ta dauka kuma a kayi ta murna da addu’a ga gwamnatin amma bincikenmu ya gano kamar rijiya ce ta bada ruwa guga ya hana.

Wa aka dauka a wancan tsarin na shelar gwamna? Nawa ke ba a dauka ba? Abin da muka gano yana da tayar da hankali.

Abin takaici ma shi ne sai akayi amfani da wannan sanarwa akace duk mai son a dauke shi aiki yaje ya sayi wani fom akan dubu goma (10,000) mutane masu dimbin yawa suka sayi fom din, wanda daga baya ya zama kamar samar da wasu kudin shiga ne a wani asusun jami’ar. Ya akayi da kudin da aka tara na wannan sayen fom na neman aiki?

Lissafin da aka bayyana mana bashi da kyau.
Jami’ar tana da asusu daban-daban wanda doka ta yarda da su, binciken dake wajen mu dukkanninsu sun shiga ja (red) mun gano ayyyuka daban-daban wadanda aka yi ba bisa ka’idar kasafin kashe kudi ba.

Da yawan biyan kudin tafiya har da tafiya har da tafiyar da bata dace da a biya mata kudi ba.

Mun kasa gane hikimar dake a cikin biyan kudi don kama wani ofis da sanya masa kaya da kuma daukar ma’aikaci a Abuja da sunan ofishin jami’ar Umaru Musa da ke Abuja.

Wanda kamar karama jami’ar nauyi ne, ba tare da la’akari ba, gida ne mai tsada kuma aka kashe kudin gaske a ofis din.

Da mun samu ganin VC din da mun ji dalilinsa na dagewa sai ya kori wasu malamai su talatin da shidda wadanda jami’ar ta dau nauyinsu sun kuma horu, suna kuma bautama jami’ar tsakaninsu da Allah. Amma ya dage zai canja aikinsu daga ma’aikatan dindin zuwa na wuchin gadi. Wanda kamar yana shirin yi masu kora da hali ne, kuma kashe jami’ar ne.

Wasu takardu dake wajen mu na ma’aikatan sashen share fagen shiga jami’a zai baka tausayi.

Ma’aikata su 28 duk ‘yan Katsina ya iske su an dauke bisa ka’ida sun bauta wa jami’ar tsakaninsu da Allah ya tarwatsa su da kyar ya amince da wasu, har yanzu takwas daga cikin su suna a cikin ukubar shi. Saboda kawai yana zargin sun rubuta takardar korafi akan matsalarsu sun aika wa gwamnan Katsina.

Har rubuta labarin nan muna bincike akan wani daki a hostel din mata da wata muhimmiyar daliba ke zaune kuma ance akan dauke wuta akai akai saboda da ita in bukatar hakan ta taso a gare ta. Wace yarinya ce wannan? don wa ake dauke wuta in zai kai mata ziyara?

Me ya sanya akayi wa wani ma’aikacin sashen kudi canjin wurin aiki zuwa kamfus din layin minista wanda ba a fara aiki da shi ba?

Wasu sun ce shawara ya bada a rika bin ka’ida a wajen kashe kudin jami’ar. Zargin mu ke neman tabbatarwa.

Wace daliba ce aka sake gyara wa jarabawa ba tare da bin ka’idar da jami’a ta gindaya ba? kuma akace ta ci har ma ta tafi hidimar bautar kasa. Bisa umurni da tsayawar mahaifinta ayi hakan?

Majiyoyi daban-daban bakin su yazo daya akan labarin amma rashin jin ta bakin mahaifin mun sakaya sunan sai gaba.

Takardun da ke wajenmu da ma’aikatan dake jami’ar da albashin su, da kuma kudin da gwamnatin iaha ke biya albashi a karon farko tun daga kafa jami’ar rashin tsari da bin diddigi zai sanya nan gaba kadan jami’ar ba za ta iya biyan albashi ba.

Bincikenmu ya gano shugabannin baya a cikin kudin albashi suke kara wasu malamai masu ziyara suna koyarwa suke daukar ma’aikatan wucin gadi na tilas har su ajiye wani abu na tsaron lalura.

A karon farko wasu malamai masu ziyara suna bin bashi. an kuma tsayar da wasu saboda ba kudin da za a biya su.

Wa yayi kwangilar wasu littafai da aka sanya a dakin karatu na jami’ar? wasu daga cikin littafan na iya jefa jami’ar cikin matsala idan masu su suka gano cewa anyi satar fasahar buga su ne, kamar yadda bincikenmu ya tabbatar mana.

Mun so muga VC muji cewa, wai da gaske ne baya kishin jami ar? Kuma wai yana fafutukar neman wani mukami a Abuja shi yasa ba ya zama? Bai damu da duk halin da jami’ar take a ciki ba?

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dabaibaye take cikin matsala. watanni kadan bayan hawan Farfesa Sanusi Mamman yana da kyau tun wuri gwamnan Katsina ya dau mataki. Kafin ta durkushu. Kamar yadda bincikenmu ya tabbatar.
Da zarar muka samu Magana da VC zamu fitar da cikakken rahoton mu da wasu takardun da muke dasu.

Muhammad Danjuma Katsina
Babban Editan Jaridun Katsina City News.jaridar taskar labarai da kuma the links.
Shine kuma jami in shiyya/ edita na jaridun education monitor.
08035904408.07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here