Bani Da Gurin Da Ya Wuce Taimakawa Matasa –Hon. Danlami Kurfi

0

Ruwan Offer: Bani Da Gurin Da Ya Wuce Taimakawa Matasa –Hon. Danlami Kurfi

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Tsohon dan majalisar tarayya wanda ya wakilci kananan hukumomi Dutsinma da Kurfi a shekarar 2015 zuwa 2019 Hon. Danlami Kurfi ya yi wani yunkuri kamar yadda ya saba wajan samawa wasu matasa guda takwas aiki a hukumar samar da hasken wutar lantarki ta KEDCO.

Da yake karin haske game da wannan kokari, tsohon dan Majalisar ya yi bayanin cewa baya da wani guri a rayuwarsa in banda taimakon matasa, ganin irin hali da kuma yanayin da matashi ke shiga idan ya rasa aikin yi.

wannan yunkuri na zuwa ne a daidai lokacin da dan majalisar ke da’awar cewa matasa sune kashin bayan duk wani cigaba da ya samu a siyasar da yake yi a kananan hukumomin Dutsinma da Kurfi saboda haka ya zama wajibi ya bada tasa gudunmawa wajan cigaban su.

“Ni a rayuwata, ba zan taba mantawa da gudunmawar da matasa suka bani ba, saboda haka nima ya kamata in bada tawa wajan gina ta su rayuwar da kuma ta sauran al’umma, bani da wani abinda zan ba su idan ba in yi masu irin haka ba” inji Hon.

Da ya juya game da matasan da suka yi nasarar samun wannan aiki da ke da wahalar samuwa a wannan lokaci, ya bayyana cewa rabonsu ya tsaga, kuma yana fatan suma wata rana za su yi abinda ya fi wanda aka yi masu, daga nan sai ya yi kira ga sauran masu irin wannan dama a wannan yankin na su, da su bada ta su gudunmawar.

Da yake zantawa da manema labarai a madadin mutane takwas din da suka samu wannan aikin a hukumar KEDCO Akilu Aminu ya bayyana cewa shekararsa goma da kammala karatun digiri, kuma tun wancan lokacin yake ta faman neman aiki, sai yanzu cikin hukumar Allah Hon. Danlami Kurfi ya sama masa wannan aiki.

“Ban san irin godiyar da zan yi masa ba a madadin saura, yadda ya faranta ran ‘yan uwana da abokan arzikin na, da ni kaina, ina rokon Allah Ya faranta masa rai shima, ya bashi abinda yake neman duniya da lahira.” Inji shi.

A cewarsa, duk da cewa Hon. Danlami baya rike da wata kujera ta siyasa ko mukami, amma idan yanzu yake neman wata dama, lallai za su nuna masa halarci, za su nuna masa cewa suma ‘ya ‘ya ne, haifafun kamar kowane da, kuma za su maida biki.

Akilu Aminu ya kara da cewa koda gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya baiwa mutane takwas aikin masu shaidar kammala digiri a lokaci guda, to irin yabo da godiyar da za a yi masa ke nan, balanta Hon. Danlami wanda baya rike da ko da kujerar mai gadi da sunan siyasa ko mukamin gwamnati.

Wadanda suka amfana da samun wannan nasara ta aikin a hukumar KEDCO sun hada da Khalid Balele Kurfi da Mannir Abdullahi da Akilu Aminu da mansir Abdullahi da Muntari Kabir da Sahabi Mansir da Aisha Isyaku Lawal da Yusuf Ahmad Muhammad tare da Aminu Ummaru

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here