BASARAKE YAYI KIRA DA A DAGE WAJEN WAYAR DA KAN AL’UMMA AKAN ILLOLIN CUTAR AMAI DA GUDAWA
Hassan Male
@ jaridar taskar labarai
Alh. Usman Bello Kankara (UK Bello) Kanwan Katsina hakimin Ketare yayi kira ga magaddan gundumarsa, limamai da sauran shugabannin al’umma da su himmatu wajen ganin an wayar da kan al’umma kan muhimmancin tsaftace jiki da muhalli domin rage yaduwae bullar cutar Amai da Gudawa.
Kanwan na Katsina yayi wannan kira ne a lokacin da yake shugabantar wani zama da magaddan gundumar da ya gudana a fadarsa dake Ketare.
Alh. Usman Bello Kankara ya jaddada bukatar dake akwai ga al’ummomi da su guji yin bahaya a sarari, sannan su tabbatar da tsabtar wuraren biyan bukatunsu a kowane lokaci, tare da wanke hannu kafin cin abinci da Kuma bayan an kammala biyan bukata, tare da yin Kira gare su day su tabbatar sun tafasa ruwa kafin suyi amfani da shi, inganta dafuwar abinci, tsabtace ‘ya’yan itatuwa kafin ayi amfani da su tare da tabbatar da ana rufe abinci a kowanne lokaci daga qudaje.
Basaraken yayi kira ga al’ummomin nasa da su bayar da rahoton bullar cutar ta Amai da Gudawa ga Asibiti mafi kusa domin daukar matakin gaugawa, sai Kuma ya shawarci masu shayarwa da su kula da muhimmancin yin allurar rigakafi a kan lokaci domin gujewa kamuwa da cututtuka.
A wani bangaren Kuma, Alh. Usman Bello Kankara yayi amfani da taron don yin kira ga magidanta da su bar yaransu mata yan’ tsakanin shekaru goma Sha biyar zuwa arba’in da Tara don yin rigakafin cutar nan ta tsinkau-tsinkau da mata kan samu a yayin haihuwa a dalilin sakacin zuwa asibiti don kula da lafiyarsu da ta abun haihuwa.
Tuni dai an gudanar da gangamin yaki da cutar tun daga ranar tara zuwa Sha ukku ga watan satumbar da muke ciki a wasu kananan hukumomi ciki har da karamar hukumar Kankara.