SHARHIN: Katsina City News
ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA
…A tabbatar Da An Yi Adalci
*Jinjina Ga Gwamnan Katsina Da Alhaji Muntari Lawal
@Katsina City News
Ranar Asabar 2 ga watan Oktoba, 2021 aka fitar a matsayin ranar da za a yi zaben shugabannin jam’iyyar APC na Jihohi.
Kwamitin riko na zaben shugabannin ya fitar da ka’idoji da kuma tsare-tsaren da ya gindaya, wadanda sune aka yi ta amfani da su a zaben shugabannin Unguwani da Kananan Hukumomi.
Har ila yau, Jihohi da yawa suna ta rikici kafin da bayan zabubbakan, wasu an shigar da kara daban-daban a kotuna, wasu na shelar za su fasa kwaryar garin don kowa ya rasa.
A Katsina cikin karfin ikon Allah komai yana tafiya lafiya lau da kudurin da Gwamna Aminu Bello Masari ya dauka, kuma yake aiwatarwa a aikace shi ne adalci.
Duk zababbunkan da aka yi, adalcin Gwamnan ya zama abin misali, wannan ya sanya jam’iyyar ta zauna lafiya a iya abin da jaridar nan ta sani.
Sallah daga Liman take gyaruwa, wannan ya sa Shugaban Kwamitin, Alhaji Muntari Lawal shi ma ya tsaya CAK a kan matsaya ta adalci, komai nasu suna yin sa ne a bude, kuma baje a bisa faifai.
‘Yan kwamitin baki dayansu da suke wakiltar ‘yan takarkari duk sun ce tafiyar su karkashin shugabancin Alhaji Muntari Lawal masha Allahu, ALHAMDULILLAH.
Yanzu kamar a ce a Sallah ce, an zo raka’ar karshe, kuma an yi Sujadar karshe, saura dagowa Sujada da Tahiya domin Sallama, Sallah ta kammalu ke nan.
Mu a jaridun Katsina City News muna kira a tabbatar da cewa, jam’iyyar APC a Katsina ta karkare da yadda ta faro a sauran zabubbakan.
Wato bin ka’idojin da aka faro da su, adalci da aiki da shi. Wannan shi ne zai gina jam’iyya mai karfi, wadda a dimokaradiyya jam’iyya ita ce ginshikin mulki.
‘Yan takara daban-daban sun fito, wasu kuma ana jiran fitowar su.
Kiran mu a kammala yadda aka faro, babu sa baki ba tursasawa ba katsaladan ba sanya ido.
A kyale kowa ya baje kwanjinsa, a kuma yi adalci.
A zabubbakan baya da Gwamna da mataimakinsa sun nuna kyakkyawan misali, abin alfahari, abin nuni, sun kuma kawo wa jam’iyyar APC kwarjini a Nijeriya.
Duk kasar nan an sanya wa Katsina ido a matsayin Jihar Shugaban Kasa, Cibiyar kulle-kullen siyasa, shin za ta kammala kamar yadda ta fara? Zabe cikin bin ka’ida, adalci da kwanciyar hankali?
A jaridun Katsina City News, wadda daya daga cikin muradin kafa ta, shi ne samar da ingantacciyar gwamnati a bisa tsarin dimokaradiyya.
Za mu sa ido daga yau 20/09/2021 zuwa 04/10/2021. Kullum za mu saki labari ko sharhi a kan zaben na shugabannin jam’iyyar APC a matakin Jiha.
Allah ya sanya a yi lafiya, a kuma yi adalci. Ameen.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 081 37777245