EFFC ta kama ɗaliban jami’a 30 da zargin zamba.
Daga: Comrade Musa Garba Augie.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC shiyyar jihar Kwara, ta ce ta cafke wasu dalibai 30 saboda zargin damfara ta intanet a jami’ar jihar Kwara,
Mai magana da yawun EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa an kama wadanda ake zargin ne bayan wani rahoton sirri kan zarginsu da hannu a zamba ta yanar gizo.
Ya ce bayan samun bayanan abun da suke aikatawa ne jami’an hukumar suka dira a wasu dakunan kwanan dalibai tare da yin bincike, lokacin ne aka kama wadanda ake zargin.