ISIS ta kashe ƴan Taliban 45 yayin sabon harin da ta kai Afghanistan.
Kungiyar IS ta yi ikirarin kai hare-hare na farko a Afghanistan waɗanda aka kai wa Taliban tun bayan da ta karbi mulkin kasar a watan Agusta.
Kungiyar reshen Afghanistan ta ce ta kai hare-haren guda bakwai a Jalalabad a ranakun Asabar da Lahadi, abun da ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun Taiban 45, da raunata wasu da dama.
Wani shaida ya ce ya ga lokacin da ake kai ‘yan Taliban da dama da suka jikkata asibiti.
Birnin wanda ke gabashin Afghanistan ya kasance wata durka ta kungiyar ISIS.
Daga: Comrade Musa Garba Augie.