JAM’IYYAR APC A MATAKIN SIRADI

0

Sharhin Taskar Labarai

JAM’IYYAR APC A MATAKIN SIRADI
Daga Abdurrahman Aliyu
@ www.jaridartaskarlabarai.com

Hausawa na kallon siradi a matsayin dayan biyu, ko dai a tsallake lafiya ko kuma akasin haka. Tabbatuwar tsallakewarka lafiya shi ne kyawawan aiki da yin abu bisa daidai gwargwadon yadda aka shardanta.

Irin wannan matakin shi ne jam’iyyar APC a Jihar Katsina take a halin yanzu, na fuskantar zaben jagororin jiha musamman wanda zai shugabanceta.

A zabukan da suka gabata a baya na gundumomi da ƙananan hukumomi a jihar Katsina an ga yadda kwamitin shirya wannan zabe suka yi adalci wajen fitar da tsarin shugabancin a dukkan matakan.

Yanzu jam’iyyar ta zo wani yanayi da ya kamata a tallafeta kar ta durkushe, domin jagoranci na daya daga cikin hanyoyin da ka iya sa a nemi Jam’iyyar a rasa ta fada a kasan siradi.

Wannan Jaridar na ganin cewa adalci shi kadai ne hanyar da za a iya bi domin tallafar jam’iyyar a jihar Katsina. Sanin kowa ne cewa gwamnan jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari mutum ne da ya tsayu wajen ganin an yi adalci a matakin jam’iyyar shi ya sanya ma ya bayar da shugaban kwamiti wanda zai iya yin tsayin daka wajen ganin ba a yi abinda ya saba doka ba a wajen zaben shugabannin jam’iyyar a matakai daban-daban.

Ya zuwa yanzu mutane masu zawarcin jam’iyyar a matakai mabambanta ana ta ganinsu da jin duriyarsu, kuma an san wadanda za su iya yi wa jam’iyyar adalci wadanda ke tare da mutane kuma mutane ke mararinsu.

A jihar Katsina kallo ne ya koma sama domin duk sauran jihohi sun sanya Ido suga ya za ta kaya a jihar, kuma suna kallon jihar a matsayin wani dan ba na tallafar jam’iyyar a matakin kasa, domin nan ne jihar shugaban kasa kuma nan ake sa ran za a samu adalci wajen fitar da shugaban jam’iyya da wadanda za su jagorance ta.

A rubutu na gaba zamu kawo maku sharhin gudumuwar da wasu jagororin da ke akai suka bayar na cigaba ko akasin haka ga jam’iyyar ta APC a tsawon lokacin da suka share a bisa karagar jagoranci.
Abdurrahman Aliyu.Dalibi ne mai karatun digri na ukku.kuma yana cikin editocin jaridar taskar labarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here