ZABEN BALA MUSAWA ZAI MAIDO MARTABAR APC DA “YA “YANTA

0

ZABEN BALA MUSAWA ZAI MAIDO MARTABAR APC DA “YA “YANTA
…….Muktar yahaya alkatsinawiyyi
@ jaridar taskar labarai
Wani matashin Dan siyasa kuma Dan jam iyyar APC’ jigo a kungiyar muryar talakka da kungiyar arewa youth progressive vanguard, yayi bayanin cewa zaben bala abu musawa a matsayin shugaban jam iyyar APC zai maido ma da jam iyyar cikakkiyar martabarta.haka kuma shugabannin jam iyya.zasu dawo da darajarsu.yan jam iyya zasu yi alfahari da jam iyyar APC.
Muktar ya rubuta wannan ne, a wani rubutu da ya aiko ma jaridun taskar labarai Wanda ya ce matsayarsa akan zaben shugabannin jam iyya da za a yi a zaben 2 ga watan oktoba mai zuwa.shine Bala abu musawa ne, mafitar jam iyyar APC.
Muktar alkatsinawiyyi Wanda kuma yake shine shugaban kungiyar Arewa progressive youth vanguard ya kara da cewa .
APC na bukatar Dan siyasa,Wanda zai yi ma siyasar bauta, Wanda kuma ya San siyasar.wanda bai da wani guri sai cigaban al umma ta siyasa da mulkin dimokaradiyya.
Muktar yace APC bata bukatar Dan kasuwa Wanda zai amfani da shugabancin jam iyyar ya Gina kanshi .ko kuma Dan boko da zai ka jam iyyar yayi cinikinta.
A yanayin da kasar ke ciki da kuma jam iyyar ta APC, bala abu musawa ne dai dai zama shugaban jam iyyar na jaha…inji alkatsinawiyyi.
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
@www.katsinacitynews.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here