Gwamna Ganduje ya naɗa sabon sarkin Gaya
Daga Ibrahim Hamisu
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da naɗin Alhaji Aliyu Ibrahim a matsayin sabon sarkin Gaya,
Sakataren Gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da hakan a cikin daren jiya Asabar a gidan gwamnatin Kano.
Sakataren gwamnatin ya ce, sahale naɗin nasa ya faru ne sakamakon shawarar sunaye uku da masu naɗin sarki a masarautar suka gabatar.
Hakan nan ya kara da cewa bayan tantance mutanen ne gwamnati ta amince da naɗa Alhaji Aliyu Ibrahim a matsayin sabon sarkin.
Alhaji Aliyu Ibrahim, shi ne babban ɗa ga marigayi sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulƙadir, kuma kafin bayyana sunansa a matsayin Sarkin na Gaya mai daraja ta ɗaya yana rike da mukamin Chiroman Gaya.
In dai ba’a manta ba a ranar Laraba 22 ga watan Satumba da muke ciki ne ne dai Sarki Gaya ya rasu wanda yana daya daga cikin sabbin sarakunan 4 da gwamna Ganduje ya kirkira.