Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya yayin wani sabon hari a Borno.

0

Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya yayin wani sabon hari a Borno.

Rahotanni daga Najeriya na cewa kungiyar Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya bakwai da ‘yan sa kai hudu, bayan wani harin kwanton bauna a tsakanin karamar hukumar Marte zuwa Dikwa a jihar Borno, da ke arewa maso gabashin kasar.

Wasu majoyoyi sun ce daya daga cikin motocin da ke cikin kwambar sojojin ce ta taka wani abun fashewa da aka binne a kasa, nan take ta tashi.

Majiyoyin tsaro sun ce jim kadan bayan fashewar ne kuma mayakan suka rika harbo manyan makamai ga motocin jami’an sojin.

Ba wannan ne karon farko da aka kashe sojojin kasar a harin kwanton bauna a yankin da Boko Haram ta yi sansani ba, don ko a watan Afrilun da ya gabata ma an kashe wasu da dama, bayan da motarsu ta taka wani bom da aka dana a karkashin kasa a jihar Borno.

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here