ME KAMFANIN GREEN HOUSE YAKE BOYEWA NE? (1)
Sharhin jaridun Katsina City News
Kamfanin da ke buga jaridun Katsina City News, jaridar Taskar Labarai da The Links da kuma mujallun Katsina City News da Matasa, sun samu wasu korafe-korafe guda hudu a kan kokarin mallakar ginin tsohuwar Ma’aikatar Watsa Labarai da ke Katsina da green house ke son yi.
Daga cikin korafin, daya ya fito ne daga ‘yan kasuwa, wadanda suke nuna ana shirin aikata abin da bai kamata ba.
Wani korafin kuma ya fito ne daga wasu dattawan Katsina da suka roki a fara rubutu da jawo hankali a kan lamarin, domin kuwa ana son rusa daya daga cikin gine-gine masu alaka da tarihin Katsina.
Daya daga cikin ginin ya fi shekaru 100, domin shi ne dakin karatu na farko, dakin taro na farko da dakin kallo don jama’a na farko.
Na biyu, dakin karatun Jihar Katsina ya yi kadan, ya tsufa, yana bukatar karin fili don fadadawa, Jihar Katsina babbar Cibiyar Ilimin addinnin Musulunci da kuma Boko da wayewar siyasa, tana da ginin dakin karatu mafi kankanta a duk Nijeriya da yammacin Afrika.
Wata takardar da muke da ita, wasu na tattaunawa da Lauyoyi domin zuwa kotu a kan dakatar da shirin mallaka wa kamfanin Green House wannan gini.
Bayan mun yi nazarin takardun da muke da su, mun tattauna da masu korafin, mun ji ra’ayin jama’a da ‘yan kasuwa, mun kuma gabatar da namu binciken.
A iya binciken da muka gudanar, mun gano Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari bai da laifi a cikin wannan aikin da ake korafi akai.
Mun fahimci cewa, Masari yana da wani irin kishi da saukin kai da zumudin ya aikata abin ci gaba da karfafa wa wanda ke neman kawo ci gaban Jihar Katsina gwiwa.
A wannan halin ba a taba samun Gwamna kamarsa ba.
Shi ne Gwamnan da zai halarci aikin ci gaba don karfafa gwiwa, wanda a tsarin aiki, Mukaddashin Darakta ne ya kamata ya je, amma shi zai je don ya karfafa gwiwa.
Gaskiyar magana Gwamnan Katsina na shan wahala, saboda wannan saukin kai, kumaji da kuma kishin irin nasa.
Bayan gano wasu abubuwa a kan yadda Green House ke kokarin mallakar wannan gini mai tarihi, sai muka fara neman jin ta bakin manyan jami’an kamfanin, yau kwanaki 37 ke nan, mun bi duk hanyar da za mu bi, amma mun kasa samun hadin kai daga gare su.
Wasikar karshe da muka rubuta wadda muka hada da rubutun nan, yau kwananta takwas (karanta abin da muka rubuta masu), ba amsa, ba magana mai dadi.
Tambayar da mu ke yi ita ce, me kamfanin Green House yake boyewa ne? Me ya sa ba ya son yin magana a kan wannan hulda marar farin jini?
Akwai yiwuwar jaridunmu su fadada bincikensu hatta a kan ginin da Green House yake sana’arsa. Shin karfin ginin ya cancanta dandazon mutane su rika shiga kamar haka suna huldar kasuwanci? Akwai dokokin kasa da kasa na kasuwanci da hulda, shin kamfanin yana bin duk wadannan dokokin?
Abin da ya kamata kamfanin Green House ya sani, kasuwanci sana’arsa ce, aikin jarida kuma ita ce tamu sana’ar. Duk dokar duniya ta yarda da bincike na adalci da rubutun a kan komai da ba da labari.
Kuma babu ruwanmu da Dan kasuwa sai ya wuce iyakar da zamu yi aikinmu na rubutu
Katsina Cibiyar Ilmi ce da wayewa. A garin Katsina ne Sarkin Katsina, Muhammadu Dikko zai je kilisa, wani talaka daidai kauyen Bakiyawa ya daga murya ya ce; “Sarki ina da tambaya”.
Mai martaba Sarki ya tsaya ya saurari talakan, ya ba shi amsa, ya yada zango a garin, ya yi Sallah, ya ci abinci, sannan ya wuce Kurmiyal.
A nan ne aka yi Shugaban kasa da bai tsoron tambaya, shi ne Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua yana Shugaban kasa, a Legas wani Dan jarida ya taso, masu tsaro suka dakatar da shi, ‘Yar’aduwa ya ce a kyale shi ya iso ya yi tambayarsa. Haka aka yi, har ma suka dau hoto tare.
Nan ne ake da Gwamnan da yanzu shi ne wanda maganarsa ta fi tambari a kasar nan, ba shi da wani abin boyewa, kuma yana iya bayyana gaskiyarsa a duk inda aka tare shi, shi ne Aminu Bello Masari.
A Katsina duk attajiranmu ba sa tsoron tambaya a kan abin da ake son jin ta bakinsu, musamman Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da Alhaji Abdul’aziz Maigoro.da matashin Dan kasuwan Alhaji Dahiru Usman sarki da sauransu
Me ya sa kamfanin Green House ba su son magana a kan mallakar ginin tsohuwar Ma’aikatar Watsa Labarai? Me suke boyewa?
Tun da mun yi kokarinmu ya ci tura, za mu fara kawo ra’ayi da rubutun mutane a kan wannan huldar da ake ta koke akanta. a jaridunmu.
Da dakin karatu na Katsina da kamfanin Green House wa ya kamata ya mallaki ginin tsohuwar ma’aikatar Watsa Labarai?
A kasar nan wace Jiha ce Dan kasuwa ke neman a rusa tsaffin gine ginensu na tarihi?
Don amfanin kansa da iyalan shi.
Me ya sa duk tsaffin ‘yan kasuwa da attajiranmu babu wanda ya taba neman a ba shi ginin gwamnati ya mayar nasa?
Mun yanke shawarar fara labarai na musamman a kan wannan hulda ta mallakar ginin tsohuwar Ma’aikatar Watsa Labarai, duk mai ra’ayinsa ya aiko zuwa ga email katsinaoffice@yaho.com, ko kuma WhatsApp 07043777779. Za mu tace, kuma za mu buga masa.
A duk shafukan mu na yanar gizo.za kuma buga a fitowar mujjalar katsina city news ta watan Nawumba.
Wannan shine matsayar jaridunmu.
Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com
07043777779.081377777245
Email. katsinaoffice@yahoo.com