KAMFANIN CONTINENTAL YA SAMU LASIN KAFA GIDAN REDIO
Muazu hassan
@ katsina city news
Shahararren kamfanin nan mai suna CONTINENTAL computers dake katsina ya samu lasisin kafa gidan rediyo a jahar katsina.
Sunan kamfanin ya fito a cikin jerin sunayen kamfanonin da shugaban kasa ya baiwa damar su kafa gidan rediyo.
A jerin sunayen kamfanin CONTINENTAL shine na 111 da aka hukumar bada lasisin gidajen talabijin da redio ta sanar.kamar yadda shugaban kasa ya amince.
Tun a shekarar 2018 a wani taro a garin kadandani.shugaban na kamfanin CONTINENTAL Alhaji salisu mamman ya sanar cewa zai kafa gidan rediyo mai gajeren zango a katsina.kuma tun a lokacin ake ta fafutukar hakan,sai a wannan shekarar 2021 Allah yayi aka samu lasisin.
CONTINENTAL computers yana cikin harkokin kasuwanci daban daban a katsina.